Hirar Waya Da Aka Bankado: Shin Na Bogi Ne Ko Kirkira Aka Yi? Lai Mohammed Ya Tambayi Peter Obi

Hirar Waya Da Aka Bankado: Shin Na Bogi Ne Ko Kirkira Aka Yi? Lai Mohammed Ya Tambayi Peter Obi

  • A karshe gwamnatin tarayya ta yi martani ga hirar waya da aka bankado tsakanin Obi da Bishop David Oyedapo
  • Da yake bayyana matsayin gwamnati kan lamarin, ministan labarai da al'adu ya ce dan takarar na Labour Party yana da tambayoyi da zai amsa
  • Alhaji Lai Mohammed ya kuma bukaci tsohon gwamnan na jihar Anambra da ya fito fili ya yi bayanin abun da yake nufi da "sautin muryar da aka bankado na bogi ne"

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, yana da karin tambayoyi da zai amsa game da hirarsu da shugaban cocin Cocin Living Faith, Bishop David Oyedapo, da aka bankado.

Bayan shafe kwanaki ba tare da ya yi magana ba, Obi ya ce sautin muryar na bogi ne, sannan ya zargi gwamnatin tarayya da yada karairayi a kansa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga A Kano Sun Bi Dare Sun Sace Wani Fitaccen Dan Kasuwa, Sun Bindige Mutum 2

Peter Obi da Lai Mohammed
Hirar Waya Da Aka Bankado: Shin Na Bogi Ne Ko Shiri Ne? Lai Mohammed Ya Tambayi Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi, Lai Mohammed
Asali: Facebook

'Sautin muryar da aka bankado, shin na bogi ne ko an shirya ne?' Lai Mohammed ya tambayi Obi

A wani taron manema labarai a Landan, ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya kalubalanci Obi da ya yi karin haske kan abun da yake nufi da 'hirar da aka bankado na bogi ne, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mohammed ya ce sautin muryar da aka bankado ya tabbatar da matsayin cewa yakin neman zaben Obi ya kasance bisa tafarkin addini da kabilanci, rahoton Punch.

Bishop Oyedepo yi yi martani a kan tattaunawarsa da Obi da aka bankado

A baya dai mun ji cewa Bishop David Oyedapo, ya yi watsi da ikirarin tattaunawa da dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi don taimaka ma sa da kuri'un Jihar Kwara gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwanaki 50 Ya Bar Aso Rock, An Yi Karar Shugaba Buhari da NBC a Kotu

Da yake jawabi a cocinsa a ran Lahadi, 2 ga watan Afrilu, babban faston na Najeriya ya ce shi bai taba tallata wani dan takara ba a fadin kasar nan.

A dai hirar tasu da Obi wanda ya karade intanet, an jiyo dan takarar na jam'iyyar LP yana neman goyon bayan faston ya taimaka masa da kuri'un kiristocin da ke kudu maso yamma da na Jihar Kwara, jihar da malamin ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng