Tirela Maƙare Da Kaya Ta Ƙwace Ta Afka Wa Masallata A Suleja Cikin Watan Ramadan
- Wata motar tirela ta kwace zuwa masallaci a Suleja inda ta danne mutum uku wanda ke asibiti karbar magani
- Shaidun gani da ido sun ce motar ta fadi ne a kokarin wucewa titin da ke a matse bayan da aka tare kasar ginin
- Wani dattijo ya shaida cewa, an yi sa'a mutane sun bar masallaci bayan idar da sallar asuba, da hadarin ba zai zo da kyau ba
Suleja, Neja - Wata trela makare da madara na gari ta kutsa kai cikin wani masallaci a Suleja, Jihar Neja, a ranar Talata, inda a kalla mutane uku suka makale, Daily Trust ta rahoto.
Hatsarin ya faru ne misalin karfe 6 na safiyar lokacin da mutane da dama sun fice daga masallacin bayan sallar Asuba.
A cewar shaidun gani da ido, tirelan ta fada a sashin baya na masallacin inda mata da yara ke sallah.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai, mutane uku, ciki har da yaro, sun makale a baraguzan kuma sun jikkata.
Da wakilin majiyarmu ya kai ziyara inda abin ya faru, ya hangi masu jimami zagaye da motar da ta fadi wanda ta rufe titin Biba da ke kasuwar Babangida.
Tirelar ta fadi bayan da take kokarin wuce siririn titin da kasa ta rufe wanda ake gina shaguna da ita.
An kai mutum uku ciki wadanda abin ya ritsa da su asibiti - shaidan gani da ido
Wani mazaunin yankin, Baba Maiunguwa, wanda ya zanta da wakilin majiyarmu, ya ce an kai mutum uku babban asibitin Suleja don karbar magani.
Ya ce:
"Hadarin ya faru bayan sallar asuba. An kai mutane uku asibiti harda karamin yaro. Alhamdulillah, ba a samu mutuwa ba.
"Mun yi sa'a mutane sun bar masallaci bayan an idar idar da sallah. Da abin yayi kamari, saboda masallaci a cike ya ke lokacin da ake sallah."
Babbar mota ta yi gobara a gadar Neja
A wani labarin daban kun ji cewa wata babbar motar dakon kaya ta yi gobara a kan gadar Neja da ke bangaren jihar Anambra.
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Juma'a kamar yadda The Punch ta rahoto, kuma hayaki ya fito daga cikin motar ya tirnike gadar.
Pascal Anigbo, mai magana da yawun Hukumar Kiyayye Haddura na Tarayya, FRSC, reshen jihar ta Anambra ya tabbatar da lamarin.
Asali: Legit.ng