Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Sace Wani Babban Basarake Da Wasu Mutane Da Dama

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Sace Wani Babban Basarake Da Wasu Mutane Da Dama

  • Miyagun ƴan bindiga sun lallaɓa cikin tsakar dare sun sace wani basarake a birnin tarayya Abuja
  • Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane da dama a sumamen da suka kai zuwa ƙauyen
  • Ba a samu asarar rai ba a harin da ƴan bindigan suka kai, sai dai wani yaro ya raunata a ƙafa

Abuja - Ƴan bindiga sun sace magajin garin ƙauyen Chida, John Kwayidami da wasu mutum 13, cikin ƙaramar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an harbi wani yaro ɗan shekara 18 a ƙafa yayin da yake ƙoƙarin guduwa.

'Yan bindiga sun sace basarake a Abuja
Miyagun 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake a Abuja Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wani mazaunin ƙauyen na Chida, Ishaya Musa, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 11:34 na dare, lokacin da ƴan bindigan ɗauke da bindigu ƙirar AK-47 suka dira cikin ƙauyen.

Kara karanta wannan

Ashsha: Yadda Aka Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android, Ya Kone Kurmus

Ya ce ƴan bindiga sun shiga gidan basaraken sannan suka yi awon gaba da shi inda daga nan suka wuce suka ƙara dauƙo wasu mutum 13 daga gidajen su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Abin takaici, wani yaro wanda ya tsorata a dalilin ƙarar harbe-harben bindiga, ƴan bindigan sun harbe shi a ƙafa yayin da yayi ƙoƙarin guduwa. Yanzu haka yana asibiti ana duba lafiyar sa." A cewarsa

Musa ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da aka sace ɗin suna barci ne a waje saboda tsananin zafin da ake fama da shi lokacin da ƴan bindigan suka dira ƙauyen suka yi masa ƙawanya.

Ya bayyana cewa an samu jin ta bakin ƴan bindigan ranar Asabar lokacin da shugaban su ya kira iyalan mutanen da suka sace.

Matsayar hukumar ƴan sanda dangane da lamarin

Kakakin rundunar hukumar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, bata tabbatar da aukuwar lamarin ba har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Ba N50m Ba: Daga Karshe 'Yan Bindiga Sun Bayyana Sharuddan Sako Mutum 85 Da Suka Sace a Zamfara

Yan Bindiga Sun Halaka Ɗan Sanda, Sun Jikkata Wasu Uku

A wani labarin na daban kuma, tsautsayi ya afka kan wasu jami'an tsaro na ƴan sanda, bayan da ƴan bindiga suka kai musu farmaki.

Ƴan bindigan sun halaka ɗaya daga cikin jami'an ƴan sandan, yayin da kuma wasu daga ciki suka samu raunika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng