"Kar Wanda Ya Kula Ta" Wani SuarayiYa Dora Hoton Budurwarsa Da Gargaɗi
- Wani matashin saurayi ɗan Najeriya ya girgiza soshiyal midiya bayan ya wallafa Hoton budurwarsa cikin alfahari a Facebook
- Da yake nuna wa duniya wacce ta sace zuciyarsa, saurayin yace ita ce mace ɗaya tilo da ta faɗa masa soyayya ba ruwanta da kuɗi
- Duk da ya tabbatar da shi talaka ne mai karamin ƙarfi, ɗan Najeriyan ya gargadi sauran maza su guji shiga gonarsa
Wani saurayi ɗan Najeriya mai suna, Aondoawase Tyofa, ya wallafa bayanan budurwarsa a shafin Facebook haɗe da sakon soyayya mai daɗi da gargadi ga sauran Samari.
Tyofa ya wallafa Hotuna biyu da suka ɗauka tare da kuma Hotunan zankaɗeɗiyar budurwar ita kaɗai, ya ce ta riga ta sace kafatanin zuciyarsa.
Ya zuba kalamai a kanta kana ya ce ita ce mace da farko a rayuwarsa da ta haska masa ya gane soyayyar gaskiyaba ruwanta da kuɗi.
Ya ce duk da ba shi da isassun kuɗi, zasu ci gaba da gina soyayya a tsakaninsu. Mista Tyofa ya ƙara da gargaɗin sauran maza da ka iya hango ta su shiga gonarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutumin ya gargaɗi sauran maza da su guje wa shiga gonar budurwarsa domin idan kunne ya ji gangar jiki ta tsira, zasu iya shiga masifa. A kalamansa ya ce:
"Barka abokai, ina mai sanarwa kowa da ke Facebook cewa wannan yarinyar da kuke gani tawa ce ni kaɗai, zuciyata ce, ita kaɗai ta faɗa mun soyayya ba ruwanta da kuɗi."
"Saboda haka duk da bani da kudi tun da muna ƙaunar junan mu zamu gina alaƙa mai kyau. Gargaɗi na shi ne, idan ka san idonka ya hango ta, to ka gaggauta ɗauke idonka tun da wuri domin zaka jawo wa kanka bala'i."
Jerin Irin Tufafin Da Aka Haramta Saka Wa A Jami'ar Calabar
A wani labarin kuma Mun haɗa maku jerin kalar tufafin da aka harmata sanya wa a Jami'ar Kalaba da ke jihar Kuros Riba
Jami'ar ta bayyana kalar kayan da ta sahalewa kowa ya sanya a cikin jami'a sakamakon yadda ta ga shiga rashin ɗa'a na karuwa.
Daraktan SERVICOM na jami'ar ne ya bayyana haka a wata sanarwa, ya nuna rashin jin daɗinsa ga halayen wasu Malamai da ɗalibai.
Asali: Legit.ng