Hukumar Alhazai Ta Sanya Wa'adin Kammala Biyan Kudin Hajjin Bana

Hukumar Alhazai Ta Sanya Wa'adin Kammala Biyan Kudin Hajjin Bana

  • Hukumar jindaɗin Alhazai ta birnin tarayya Abuja ta bayyana ranar kammala biyan kuɗin Hajjin bana
  • Hukumar tace saɓawa hakan ka iya janyowa maniyyata matsala wajen tafiya zuwa ƙasa mai tsarki
  • A cewar hukumar maniyyatan da suka kammala biyan kuɗinsu akan kari suna da wata garaɓasa ta daban

Abuja- Hukumar jindaɗin Alhazai ta birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa maniyyatan bana na birnin tarayya Abuja da suka fara biyan kuɗin Hajjinsu, suna da daga nan zuwa ranar 21 ga watan Afrilu domin kammala biyan kuɗin.

NAHCON a ranar Juma'a ta sanar da cewa maniyyatan bana daga birnin tarayya Abuja za su biya N2,919,000 a matsayin kuɗin Hajjin bana, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

NAHCON
Hukumar Alhazai Ta Sanya Wa'adin Kammala Biyan Kudin Hajjin Bana Hoto Daily Trust
Asali: UGC

Wata sanarwa daga kakakin hukumar Muhammad Lawal Aliyu, ta bayyana cewa wa'adin an sanya shi ne domin ba hukumar damar cika wa'adin da NAHCON ta sanya dukkanin jihohi da birnin tarayya domin kammala biyan kuɗin aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Sansanin Yan Gudun Hijira a Arewa, Sun Kashe Mutane Sama da 40

Sanarwar tayi bayanin cewa cikata ragowar kuɗin zai ba hukumar damar kammala haɗa jerin sunayen maniyyatan bana, duba da cewa lokacin fara jigilar maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki na ƙara ƙaratowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa biyan cikon kuɗin zai sanya hukumar ta cigaba da sauran shirye-shiryen tafiya da kuma cika umurnin wa'adin da NAHCON ta sanya domin kammala biyan kuɗin hajjin bana.

Kakakin ya kuma jaddada cewa waɗanda kawai suka kammala biyan kuɗin zuwa ranar wa'adin ne, za a sanya sunayensu a cikin jerin sunayen maniyyatan bana.

Akwai garaɓasa ga waɗanda suka kammala biyan kuɗin su

Ya kuma ƙara da cewa bayan maniyyatan sun kammala biyan kuɗinsu, za a ba su damar zaɓar jirgin da suke son ya kai su ƙasa mai tsarki lokacin jigila, rahoton jaridar Independent

Yayi bayanin cewa za a cigaba da wayar da kan maniyyata a ranakun 29 da 30 na watan Afirilu, a sansanin Alhazai na dindindin da ke a Bassan Jiwa kusa da tashar filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe.

Kara karanta wannan

An Samu Ƙari: Daga Karshe An Bayyana Kuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023, Ta Kasu Zuwa Gida 8

NAHCON Ta Sanar da Kuɗin Kujerar Sauke Farali, Ta Raba Su Zuwa Kaso 8

A wani labarin na daban kuma, hukumar NAHCON ta bayyana kuɗin zuwa ƙasa mai tsarki domin aikin Hajjin bana.

Hukumar ta raba kuɗin Hajjin bana zuwa rukuni 8, inda ko wane rukuni kuɗinsu daban za su biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng