'Yan Sanda Sun Sheke ’Yan Bindiga 2 a Zamfara, Sun Raunata Wani Adadi Mai Yawa
- Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi babban aiki, ta hallaka ‘yan bindiga a wani aikin dakile harin tsageru da ta yi
- Rahoto ya bayyana cewa, an kashe ‘yan bindiga biyu tare da raunata da dama a harin na karamar hukumar Tsafe
- A karshen mako, rundunar ‘yan sanda ta kame wasu tsagerun ‘yan daba a wani yankin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas
Jihar Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun dakile wani mummunan harin da wasu tsagerun ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Tsafe ta jihar.
Kakakin rundunar, Mohammed Shehu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 9 ga watan Afrilu, ya ce an kuma sheke wasu ‘yan bindiga biyu yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Shehu ya ce Kolo Yusuf, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yabawa jami’an rundunar bisa namijin kokarin da suka yi, ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su hada kai da jami’an tsaro a kokarin tabbatar da tsaro a jihar, rahoton The Cable.
Jawabin rundunar ‘yan sandan Zamfara
Da yake jawabi a cikin sanarwar:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Kolo Yusuf psc, ya yaba da kokarin rundunar ‘yan sanda da sojojin da aka tura domin dakile barnar ‘yan bindiga da sauran miyagun ‘yan ta’adda a jihar.”
A bangare guda, kwamishinan ya yiwa mazauna jihar alkawarin tabbatar da kokari da ci gaba da yakar ‘yan ta’addan da suka addabi jihar da ke Arewa maso Yamma, rahoton Channels Tv.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fuskantar matsalolin hare-haren ‘yan bindiga da masu sace mutane da neman kudin fansa.
An kama ‘yan daba a jihar Bauchi
A wani labarin, kunji yadda ‘yan sanda suka kame wasu tsagerun ‘yan daba a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin kasar nan.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kammala zabukan kasar nan, inda aka ce matasan ana zargin ‘yan daban Sara Suka ne da ke addabar al’ummar jihar ta Bauchi.
Ya zuwa yanzu, kwamishinan ‘yan sanda ya ce za gurfanar da matasan, inda ya yi kira ga iyayen yara da su kasance masu yiwa ‘ya’yansu tarbiyya mai kyau.
Asali: Legit.ng