Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe ASP Tare da Raunata Wasu Jami’ai a Shingen Bincike a Legas
- An kashe wani dan sanda tare da jikkata wasu jami’ai da yawa a wnai yankin jihar Legas da ke Kudu maso Yamma
- Wannan ya faru ne bayan da wasu ‘yan ta’adda suka hallaka ‘yan sanda a wata unguwa da ke jihar ta Legas
- ‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, sun bayyana matakin da suke dauka a halin da ake ciki
Jihar Legas - Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sheke ASP na ‘yan sanda tare da jikkata wasi jami’ai a wani farmakin da suka kai kan tirken binciken jami’an da ke Ikorodu a jihar Legas.
An kuma ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun tsere da bindigogi biyu na ‘yan sandan da aka ce sun tsaya a magamar Enure da ke Itokin a kusa da babban titin Ikorodu zuwa Abeokuta.
An tattaro cewa, lamarin ya faru ne a daren Juma’a, kasa awanni 48 kenan bayan da ‘yan bindigan kashe mazauna uku na unguwar Gowon da ke Ipaja kana kasa da awanni 24 da hallaka ‘yan sanda uku a wani yankin jihar Edo.
Yadda lamarin ya faru
Majiya ta shaidawa jaridar The Nation cewa, ana zargin wasu matsafa ne suka kai harin, wadanda aka ce sun dauki lokaci suna barna a yankin na Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, an gano cewa, akalla mutane hudu wadannan matsafa suka kashe a yankin Ikorodu, inda aka ce suna aiki ne ga wani mai kwace filayen jama’a.
Wata majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
“Matsafan na nan a Emuren kuma sun yi kaurin suna. Suna yiwa wani fitaccen mai kwace filayen jama’a aiki ne a Ikorodu.”
Maranin ‘yan sanda
A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace ana ci gaba da bincike a kai.
A cewarsa, ba za a bayyana sunaye da bayanan ‘yan sandan da suka mutu ba sai har an sanar da ahalinsu yadda ya dace.
Ya kuma tabbatar da cewa, an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannun a kisan da aka yi a unguwar Gowon a ranar Laraba da dare.
Ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis, kuma sun tabbatar da suna da hannu a barnar da ta auku.
A jihar Bauchi kuma an kama wasu matasa da ake zargin ‘yan daba ne da suka addabi jama’a a jihar.
Asali: Legit.ng