Tsohon Alkalin ICJ, Bola Ajibola, Ya Koma Ga Mahallincinsa Yana Da Shekaru 89

Tsohon Alkalin ICJ, Bola Ajibola, Ya Koma Ga Mahallincinsa Yana Da Shekaru 89

  • Mai shari'a Bola Ajibola, tsohon alkali a kotun kasa da kasa na masu manyan laifuka, ICJ, ya rasu a ranar Lahadi, 9 ga watan Afrilu
  • Mai shari'a Ajibola wanda ya rasu yana da shekaru 89 a duniya, ya taba rike mukamin Antoni Janar na Najeriya
  • A cewar sanarwar da ta bazu a dandalin sada zumunta, tsohon AGF din ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya mai tsawo saboda tsufa

Abeokuta, Jihar Ogun - Allah ya yi wa tsohon alkalin kotun kotun kasa da kasa, Hague, da ke Netherlands, Prince Bola Ajibola, rasuwa.

Ajibola, wanda kuma tsohon Antoni Janar ne na Najeriya, ya rasu yana da shekaru 89 a duniya, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Prince Ajibola
Tsohon Alkalin ICJ, Bola Ajibola, Ya Koma Ga Mahallincinsa Yana Da Shekaru 89. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

An samu tangarda: Saurayi ya fusata, ya kone gidan su tsohuwar budurwarsa kurmus

Ajibola, wanda ya kafa Jami'ar Crescent da ke Abeokuta, ya rasu a ranar Lahadi tsakar dare bayan ya dade yana fama da rashin lafiya sakamakon tsufa.

Babban dan tsohon marigayin alkalin, Segun Ajibola, SAN, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Ya rubuta:

"Cike da alhini da godiya ga Allah madaukaki.
"Mahaifinmu, Prince Bola Ajibola, ya bar duniya cikin dare. Allah ya jikansa da Aljanna Firdaus."

Takaitaccen tarihin ayyukan marigayi Bola Ajibola

Ajibola ya rike mukamin ministan shari'a daga 1985 zuwa 1991 karkashin gwamnatin mulkin soja ta Ibrahim Badamasi Babangida.

Daga 1991 zuwa 1994, ya yi aiki a matsayin alkali na kotun kasa da kasa a Hague, Netherlands.

An kuma nada Ajibola a matsayin jakadan Najeriya a Birtaniya daga 1999 zuwa 2002.

Ya kuma rike mukamin shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA, na tsawon shekara daya.

Shi ne wanda ya kafa Jami'ar Crescent da ke Abeokuta a Jihar Ogun.

Kara karanta wannan

"Dan Allah Ka Mana Alfarma Ɗaya Tak" Tsohon Minista a Najeriya Ya Aike da Sako Ga Peter Obi

Ajibola ya rasu ne shekaru bakwai bayan rasuwar matarsa Olufunmilayo, a Landan.

Tsohon shugaban yan sandan Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Mustapha Balogun, tsohon sufeta janar na rundunar yan sandan Najeriya, ya riga mu gidan gaskiya.

Vanguard ta rahoto cewa majiya daga iyalansa ta tabbatar da mutuwarsa, tana mai cewa ya rasu ne a daren ranar Alhamis.

An haifi Tafa Balogun ne a ranar 8 ga watan Agustan 1947.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164