Wani Fasto Dan Kasar Gambiya Ya Tsere Da Wayoyi 52 Da Kudi Bayan Yi Wa Mutane Wa'azi A Ibadan
- Yan sandan Jihar Oyo sun ayyana Fasto Owen Abraham a matsayin wanda ake nema bayan ya gudu da wayoyi 52 bayan gudanar da addu'a
- Wanda abin ya shafa sun ce, Faston ya umarci su ajiye wayoyin don gudanar da addu'ar
- An manne hotunan malamin a makwabtan wurare don taimakawa wajen kama malamin
Oyo, Ibadan - Mazauna unguwar Aponrin a Agbowo, Ibadan, sun bada labarin batan wayoyinsu bayan addu'a da Fasto Owen Abraham ya gudanar.
A rahoton The Nation, akalla wayoyi kirar Android da IPhone 52 na wanda suka je taron addu'ar kwanaki biyar ake zargiin Fasto Abraham ya gudu da su.
Wasu daga cikin wanda abn ya shafa sun ce malamin ya ce Allah ya turo shi daga Gambia zuwa Ibadan don gudanar da addu'ar.
Su ka ce malamin yayi ikirarin cewa ubangiji ne ya umarci da su kawo wayoyi da sauran kayayyaki, wanda ya gudu da su daga baya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mrs Grace Akintola, daya daga cikin wanda abin ya shafa ta bayyana abin da ya faru, ta ce:
"Wani dan unguwarmu ne ya gayyace ni addu'ar; mai addu'ar ya sanya kayan Fasto, ya ce zai siyawa mutum daya gida, ya ce gidan an zuba kayan ado."
Mrs Akintola, wadda bazawara ce a cewar Vanguard, ta ce:
"Ya yi alkawarin kudi ga wasu daga cikin mahalarta taron, ko yan siyasa ba za su iya bada kudin da ya alkawarta ba."
"Ranar karshe na addu'ar, ya siyar mana da jarkar ruwa akan ₦4,800. Ya ce turare ne a cikin robar ruwan, mutane da yawa sun siyi ruwan."
Wani dalibin jami'ar Abuja da ya boye sunansa, shi ma abin ya rutsa da shi, ya ce:
"Ya ce kada wayar da ta yi kara. Shiyasa ya karbi duk wayoyin, a takaice, wata budurwa ta tashi don yin hoto da shi. Ya kwace wayarta."
"A matsayinsa na malami, mun girmama shi sosai, ba mu san amfani zai yi da Allah ya cuce mu ba."
Yan sanda na neman Faston da ake zargi ruwa a jallo
A daya bangaren, rundunar yan sandan Jihar Oyo, ofishin Bodija, sun ayyana malamin a matsayin wanda ake nema bayan samun rahoto.
Yan sanda sun roki mazauna yankin da su taimaka da duk wanj bayani da zai taimaka wajen kama malamin da ake zargi.
Hotuna dauke da hoto da sunansa na zagaye da yankin don taimakawa wajen kama shi.
An kama Fasto da ya yi garkuwa da kansa don karbar kudin fansa daga mabiyansa a Filato
A wani rahoton kun ji cewa yan sanda sun kama wani fasto da ke zaune a jihar Filato kan laifin yin karyar garkuwa da kansa ya kuma karbe makuden kudaden fansa daga hannun mabiyansa.
Asali: Legit.ng