Muhawara Kai Tsaye A Talabijin: Datti Ya Amince Da Kalubalen Soyinka, Ya Aika Sako Mai Karfi
- An take wasa, gaga tawa tsakanin Farfesa Wole Soyinka da magoya bayan Peter Obi ta fara
- Kungiyar Obi-Datti a ranar Asabar, 8 ga Afrilu, ta shaida cewa dan takarar mataimakin shugaban kasar LP, Datti Baba-Ahmed, zai yi muhawara da marubucin
- Wannan martani ne ga Farfesa Wole Soyinka kan bukatar muhawara da dan takarar mataimakin shugaban kasa na LP akan sakamakon zaben shugaban kasa na 2023
Kungiyar Obi-Datti ta jam'iyyar LP ta ce dan takarar mataimakin shugaban kasarta, Datti Baba-Ahmed, ya shirya tsaf don yin muhawara da Farfesa Wole Soyinka, kamar yadda shararren marubucin ya bukata.
Idan za a iya tunawa Legit.ng ta ruwaito wanda ya lashe kyautar Nobel ya kalubalanci Datti da su yi muhawara akan sakamakon zaben 2023 wanda hakan ya janyo zazzafar suka tsakanin Soyinka da magoya bayan Peter Obi da aka fi sani 'Obidients'.
Mai magana da yawun kamfen din shugaban kasa na Obi-Datti, Farfesa Chris Nwakobia, ranar Asabar, 8 ga watan Afrilu, lokacin wata tattaunawa a Arise TV, ya amince da kalubalen.
Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Eh, tabbas zai yi. Daga cikin magoya bayan Peter Obi akwai za su iya muhawarar su kuma yi yada ya kamata."
Da yake magana kan jam'iyyar LP da amincewa da kalubalen Datti, Farfesa Nwakobia ya bayyana kalubalen Soyinka a matsayin kuri kuma ya ce marubucin ba zai halarci muhawarar ba.
Ya ce:
"Na san Farfesa Wole Soyinka, na san ba zai je muhawarar ba saboda tarihi na tafiya da batun gaskiya da kuma adadi."
Farfesa Soyinka na shan zazzafar suka daga magoya bayan Peter Obi, kuma marubucin ba zai so kasa kare kansa ba.
Kwanan ya bayyana magoya bayan Peter Obi a matsayin marasa tarbiyar magoya bayan siyasa da ya taba gani, ya na mai cewa halin su yana rage ingancin dan takararsu (Peter Obi) a siyasance.
Peter Obi da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo sun hadu a Anambra
A baya wani rahoto ya zo cewa Mista Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ya gamu da Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya a garin Awka, babban birnin jihar Anambra.
Asali: Legit.ng