Wani Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba Kuma Ya Sace Wayarta

Wani Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba Kuma Ya Sace Wayarta

  • Wani mutum ya damfari wata yar karuwa, ya hana ta kudi bayan biyan bukatarsa tare da guduwa da wayar ta
  • Bayan gurfanar da shi a gaban kotu ya musanta tuhumar da aka gabatar, sai dai kotu ta tura shi gidan yari kafin a yi nazarin hujoji da aka gabatar a kansa
  • Lauyan mai kara ya bayyana cewa wanda ake karar an yi ciniki cewa zai biya ₦2000 amma bayan biyan bukatarsa ya hana kudin

FCT, Abuja - Wata kotu da ke zamanta a Dei-Dei, Abuja, ranar Alhamis ta bada umarnin a tsare mata wani mai shekara 30, Victor Emeka, a gidan gyaran hali bisa zargin cutar wata yar gidan magajiya, rahoton The Punch.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya ruwaito dan sanda mai gabatar da kara ya tuhumi Emeka da ke Mpape, Abuja, da laifin zamba cikin aminci wanda ya musanta.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Yan Sandan Najeriya.
Wani Mutum Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Ya Sace Mata Waya. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alkalin kotun, Saminu Suleiman, ya bada umarnin a mika wanda ake zargi gidan ajiya da gyaran hali zuwa 5 ga watan Mayu da za cigaba da shari'a.

Tun da farko, lauyan mai kara, Chinedu Ogada, ya shaida wa kotu cewa mai kara, Sandra Orogbo, da ke Otal din White House, Abuja, ta shigar da kara ofishin yan sanda da ke Zuba ranar 17 ga watan Maris.

Ogada ya bayyana cewa wanda ake karar ya je otal din, ya kuma yi ciniki da mai karar kan zai biya ₦2000 kudin aikinta a ranar 16 ga watan Maris.

Ya kara da cewa bayan mai kara ta biya bukatar wanda ake kara, sai yaki biyanta.

Ogada ya ce daga nan ya yaudari mai karar zuwa Suleja, ya kuma karbe mata wayar ta na ₦60,000 ya gudu.

Kara karanta wannan

Malamin Addini Ya Ci Gyaran Abba Gida-Gida, Ya Fadi Yadda Gwamna Zai Karbe Fili

Ya kara da cewa an kama wanda ake kara kuma an mika wa yan sanda don bincike kan laifin, wanda ya ce, ya saba da sashe na 265 da 287 na kundin Penal Code.

Wani ya damfari kwarariyar karuwa ya tura mata alat din bogi bayan sun gama 'harka'

A wani labarin daban, jami'an hukumar NSCDC a Ondo sun gurfani da wani Samuel Oni a kotu kan zarginsa da damfarar wata karuwa mai suna Blessing Olaitan.

Kamar yadda The Punch ta rahoto, Olaitan wacce ta kira kanta kwarariyar karuwa, ta ce Samuel ya same ta ya biya bukatarsa kuma ya karba N80,000 daga hannunta da sunan zai mata tiransifa har da karin N15,000 amma ta ji shiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: