Neman Kudin Shiryawa Mahaifiya Ta Jana'iza Na Alfarma Ya Sa Ni Fashi Da Makami, Wanda Ake Zargi

Neman Kudin Shiryawa Mahaifiya Ta Jana'iza Na Alfarma Ya Sa Ni Fashi Da Makami, Wanda Ake Zargi

  • Wani mutum mai shekaru 24 da ake zargi ɓarawo ne ya shiga hannun bayan kama shi dumu-dumu a wani shago
  • Mutumin ya bayyana cewa ba shi da wani zabi in ba haka ba saboda ya na so ya shiryawa mahaifiyarsa jana'iza ta alfarma a matsayinsa na dan fari
  • Jami'an sintirin da suka kama shi sun bayyana yadda suka kama shi da tarin layukan waya da kuma wayoyi da dama, tare da bayyana cewa zasu mika shi ga yan sanda

Jihar Delta - Wani da aka kama bisa zargin sata a wani yanki a Delta, Emmanuel Chinagorom ya ce a kokarin shirya wa mahaifiyarsa jana'iza ta alfarma ya fada laifin.

Jaridar Punch ta ruwaito Chinagorom ya amsa laifin lokacin da jami'an sintirin Agbor Gha-Ihun suka kama shi a yankin Agbor, Jihar Delta.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ya Gwangwaje Wani Tsoho Mai Tura Baro Da Sha Tara Ta Arziki, Bidiyon Ya Tsuma Zukata

Yan Sanda
Shiryawa Mahaifiya Ta Jana'iza Na Alfarma Ya Sa Ni Fashi Da Makami, Wanda Ake Zargi. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Punch ta ruwaito mai shekara 24 ya kware a satar waya da sauran kaya masu daraja a Agbor da kewaye.

Rahotanni sun bayyana aka kama shi dumu-dumu a wani shago da ke yankin aka kuma mika shi ga jami'an sintiri.

Neman Kudin Birne Mahaifiyata Yasa Na Yi Sata, Wandaa Ake Zargi

Da ya ke zantawa da manema labarai, wanda ake zargin haifaffen Abia ya ce shi mai gyaran wuta ne amma ya koma sata saboda babarsa da ta mutu, "wadda gawarta ke kwance a dakin adana gawa, jana'iza ta alfarma a matsayinsa na dan fari."

"Ina shiga shaguna a matsayin wanda zai yi siyayya amma buri na in saci kaya masu daraja kamar salula. Wannan ne karo na farko a Agbor kafin a kama ni," a cewarsa.

Kara karanta wannan

'Jam'iyyar APC da Mambobin Majalisa Sun Nuna Wanda Suke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai'

Chinagorom ya kuma bayyana yadda ya ka hada kai da wani dan arewa mazaunin Asaba wanda ke siyan wayoyin sata, inda ya ce ya zabi sata ne saboda ba shi da mai taimaka masa.

Shugaban Sintiri Ya Ce Za A Mika Wanda Ake Zargin Hannun Yan Sanda

Shugaban yan sintiri na Agbor Gha-Ihun, Kwamared Monday Kiyem, ya shaida wa yan jarida cewa "za su cigaba da tabbatar da zaman lafiya a Agbor da kewaye don dakile masu laifi irin wanda suka kama."

Shugaban yan sintirin ya ce a binciken da suka yi, sun samu layukan waya da wayoyi da yawa a hannun sa kuma da aka kira masu wayoyin sun bayyana idan aka sace musu wayar a wuri daban daban.

Ya ce:

"Wasu daga ciki da ke Agbor sun zo ofis domin tantance wayoyinsu tare da bada labarin yadda aka musu satar.
"Zan mika Emmanuel a hannun yan sanda don cigaba da bincike da kuma zakulo abokan aikinsa a hukunta su."

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Delta kan harkokin tsaro, Kwamared Kiyem, ya shawarci masu sha'awar aikata laifi da su bar garin Agbor ku su fuskanci fushin shari'a idan suka shiga hannu.

An Damke Yan Kungiyar Ta'addanci Da Ke Tada Wa Yan Nasarawa Da Abuja Hankali

A bangare a guda, kun ji cewa yan sanda a Abuja sun yi damke wasu mambobin wata kungiya da ake zarginsu da kai hare-hare a jihar Nasarawa da Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164