NAHCON Ta Sanar da Kuɗin Kujerar Sauke Farali, Ta Raba Su Zuwa Kaso 8
- Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin bana 2023
- Shugaban NAHCON, Zikrullah Hassan, ya ce kuɗin aikin Hajji ta tashi ne sakamakon tashin farashin kayayyaki a Najeriya da Saudiyya
- Ya ce kuɗin kujerar hajji ya rabu zuwa kashi 8 kuma an samu banbani ne sakamkon kusancin wasu jihohi da ƙasa mai tsarki
Abuja - Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da kuɗin kujerar aikin Hajji ga duk maniyyacin da ke shirin sauke Farali a shekarar 2023.
Shugaban NAHCON, Zikrullah Hassan, shi ne ya bayyana haka ranar Jumu'a, ya ce kuɗin Hajjin bana ya tashi zuwa miliyan N2,89m sakamakon tashin farashin kaya a Najeriya da Saudiyya.
Hassan ya ce farashin kujerar zuwa Hajjin ta kasu zuwa kaso 8, jihohin Borno da Yola ke da farashi mafi sauƙi yayin da Legas da Ogun farashinsu ya fi tsada miliyan N2.99m.
Daily Trust ta rahoto cewa an samu ƙarin sama da dubu N300,000 idan aka kwatanta da kuɗin kujerar Hajjin bara 2022.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda farashin kujerar Hajji ta kaso zuwa gida 8
Shugaban NAHCON ya ce:
"Kuɗin aikin Hajjin bana ya kasu zuwa farashi 8, maniyyata daga Maiduguri da Yola zasu biya miliyan N2,890,000, sauran jihohin arewa kuma zasu biya N2,919,000."
"Kudancin Najeriya na da farashin kujerar Hajji kala shida, maniyyatan Edo da sauran jihohin kudu maso kudu da kudu maso gabas zasu biya N2,968,000, jihohin Ekiti da Ondo zasu biya N2,880,000, maniyyatan jihar Osun zasu biya N2,990,000."
"Maniyyata daga jihar Kuros Riba zasu lale kuɗin kujera miliyan N2,943,000, sai kuma masu niyyar sauke farali bana daga jihohin Legas, Ogun da Oyo zasu biya miliyan N2,999,000."
- Zikrullah Hassan.
Ya kuma ƙara da bayanin cewa banbancin kuɗin kujerar hajji ya faru ne saboda jihohin arewa sun fi kusa da ƙasar Saudiyya fiye da jihohin kudu. Haka nan wurin zaman da kowace jiha ta kama ya taka rawa wurin yanke farashin.
Hassan ya ce hukumar NAHCON, bayan zama da jami'an hukumar jin daɗin Alhazai na jihohi, ta amince da rufe shafin masu biyan kuɗin hajji ta hanyar shirin ajiya yau Jumu'a.
Bugu da ƙari, ya ce sun cimma matsaya cewa duk wani maniyyaci ya kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga nan zuwa 21 ga watan Afrilu, 2023, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Duk Wanda Zaben 2023 Bai Masa Daɗi ba Ya Hakura Ya Tari Gaba, Sanata Adeyemi
A wani labarin kuma Sanatan APC Ya Yi Magana Kan Sahihancin Zaben 2023, Ya Aike da Sako Ga Atiku da Obi
Sanata Smart Adeyemi ya bayyana cewa zaben da aka kammala ya fi sauran na baya da aka taɓa shiryawa sahihanci a tarihi.
Sanatam ɗan asalin jihar Kogi ya baiwa manyan yan takara da sha kaye a zabe su rungumi kaddara su jira zuwan 2027.
Asali: Legit.ng