A Cikin Ramadan Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Sun Sace Matafiya

A Cikin Ramadan Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Sun Sace Matafiya

  • Miyagun maharan yan bindiga sun kai mummunan hari ga matafiya a titin Kaduna zuwa Abuja a wani gari da ke kusa da Kagarko
  • Shuaibu Yahaya, wani mazaunin garin wanda gidansa ke kusa da inda abin ya faru ya ce maharan sun fasa tayoyin motoccin matafiyan ne kafin suka rika bi suna kwashe su zuwa daji
  • Madakin Jinjila, Samaila Babangida shima ya ce an kira ne daga garin Kagarko an sanar da shi afkuwar harin amma ba zai iya tantance adadin mutanen da abin ya shafa ba

Jihar Kaduna - An sace matafiya da dama bayan yan bindiga sun bude wa motocci wuta a garin Iche, mai nisanta wasu yan kilomita daga garin Kagarko da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, wani mazaunin unguwar, Shuaibu Yahaya, ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 7 na yammacin ranar Laraba jim kadan bayan an sha ruwa.

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi Yayin Da Mutane Da Dama Suka Yi Batar Dabo Sakamakon Mummunan Hadarin Jirgin Ruwa A Bayelsa

Taswirar Jihar Kaduna
Mahara sun tare matafiya a hanyar Kaduna zuwa a Abuja cikin watan Ramadan. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Wani mazaunin garin da abin ya faru ya yi bayani dalla-dalla

Shuaibu ya ce yan bindigan, dauke da bindigu kirar AK-47, sun harbi tayoyin motoccin don sace su, sannan suka rika zuwa mota zuwa mota suna tafiya da fasinjoji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa:

"Karar harbin bindigan su ya janyo hankali na saboda gida na ba shi da nisa da wurin da abin ya faru. Yayin da wasu motocci sun fada tarkonsu, wasu da dama sun juya cikin gaggawa sun tsere."

Basaraken gargajiya ya tabbatar da lamarin

Madakin Janjala, Samaila Babangida, shima ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa:

"A safiyar yau (jiya), an kira ni daga Kagarko cewa yan bindiga sun sace wasu fasinjoji a daren jiya, yan kilomita kadan daga garin Kagarko, amma ban san ainihin adadin wadanda aka sace ba."

Kara karanta wannan

Rashin daraja: Bidiyon dalibai sadda suke yiwa lakcara isgili don ya zo da balkwatacciyar mota

Mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna bai riga ya fitar da sanarwa kan afkuwar lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.

Yan Sanda Sun Kama Yan Kungiyar Ta'addanci Da Ke Fitinar Mutanen Nasarawa Da Abuja

A wani rahoton kun ji cewa yan sanda a Abuja sun yi nasarar cafke mambobin wata kungiya da ake zargin su da fitinar mutanen jihar Nasarawa da FCT, Abuja.

Sadiq Abubakar, kwamishinan rundunar yan sandan FCT ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wani otel dake unguwar Masaka ta jihar Nasarawa kusa da Abuja, kamar yadda rahoton The Cable ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164