Dakarun Sojoji Sun Lalata Haramtattun Matatun Man Fetur a Niger Delta
- Dakarun sojojin Najeriya sun mamayi matattarar ɓarayin man fetur inda suka lalata su
- Dakarun sojojin sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur da ɓata gari ke amfani da su a yankin Niger Delta
- Dakarun sojojin sun kuma kwato kayyayyakin aiki da dama daga hannun ɓata garin ciki har da makamai
Abuja- Hedikwatar Rundunar Tsaro (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji sun lalata haramtattun matatun man fetur 50 a yankin Niger Delta a cikin makonni biyu.
A wata sanarwa ranar Alhamis, Musa Danmadami, Darektan Watsa Labarai na rundunar, ya bayyana cewa dakarun sun kuma lalata kwale-kwalen katako 22, tankokin ajiyar mai 237, madafa 204, da ramuka 30 da ake amfani da su wajen satar man fetur ɗin, rahoton The Cable
Ya bayyana cewa dakatun atisayen Operation Delta Safe, tare da haɗin gwiwar atisayen Octopus Grip atisayen UDO KA, sune suka gudanar da wannan aikin a cikin garuruwa, bakin rafuka, hanyoyin ruwa, birane da manyan kogunan jihohin Bayelsa, Delta, Cross River, da Rivers.
Danmadami yace dakarun sun kwato litar man fetur 797,000, litar man iskar gas 276,000, litar kalanzir 500, injina guda huɗu, babura guda shida da keke mai ƙafa uku, makamai guda takwas da harsasai daban-daban, rahoton PM News
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin rundunar ga kuma ƙara da cewa dakarun sun kuma kwato wani babban inji, janaretoci biyu da wani kwale-kwale na zamani, sannan sun kuma cafke ɓata gari 26 a cikin wannan lokacin.
“Dukkanin kayayyakin da aka ƙwace da waɗanda aka cafke daga yankin an miƙa su hannun hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakan da suka dace." Inji shi
"Yana da kyau a sani cewa kuɗin da suka kai naira N407.5 aka kwace daga hannun ɓarayin man fetur ɗin."
Dakarun Sojojin Najeriya Sun Murkushe Yan Ta'adda Sama da 100 a Yankin Arewa
A wani labarin na daban kuma, dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar murƙushe ƴan ta'adda da dama a yankin Arewacin Najeriya.
Dakarun sojojin sun samu nararar ƙarar da ƴan ta'adda sama da mutum ɗari a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma cikin sati uku.
Asali: Legit.ng