Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Basarake Mai Martaba a Jihar Filato

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Basarake Mai Martaba a Jihar Filato

  • Tsagerun 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin Chip, karamar hukumar Pankshin a jihar Filato
  • Rahotanni sun nuna cewa Basarakin na da matuƙar daraja a yankin da yake jagoranta kuma maharan sun sace shi har cikin fadarsa
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan Filato, DSP Alabo, ya ce tuni jami'ai suka bazama farautar yan bindigan

Plateau - Miyagun 'yan bindiga sun sake yin awon gaba da wani babban Sarki mai martaba daga cikin fadarsa a jihar Filato da ke arewa ta tsakiya a Najeriya.

Basaraken da ya shiga hannun masu garkuwa, His Royal Highness Sunday Dajep, shi ne babban hakimin yankin Chip, garin da ƙabilar Mhiship ke rayuwa a ciki a ƙaramar hukumar Pankshin, jihar Filato.

His Royal Highness Sunday Dajep.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Basarake Mai Martaba a Jihar Filato Hoto: leadership
Asali: UGC

Daily Trust ta fahimci cewa an yi garkuwa da mai martaba Sarkin da misalin ƙarfe 11:00 na dare lokacin da 'yan bindiga sun kutsa ta tsiya cikin fadarsa da ke garin Chip, gefen titin Mangu-Shendam.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Gama Shirin Janye Tallafin Fetur, An Karbo $800m Daga Bankin Duniya

Wata majiya a cikin iyalan da ke zaune a garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace sun ji karar harbe-harbe a fadar Basaraken da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya ƙara da cewa bayan karar tashin bindigan ne maharan suka yi awon gaba da Basaraken, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka na ceto Sarkin?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce hukumar 'yan sanda ta samu labarin garkuwa da Basaraken.

A kalamansa, kakakin 'yan sanda DSP Alabo ya ce:

"Jami'an hukumar 'yan sanda sun bazama neman 'yan bindigan da suka aikata wannan ɗanyen aiki."
"Muna samun kiran gaggawa kan abinda ya faru take muka kaddamar da farautar 'yan bindigan don ceto basaraken da kame su."

Kara karanta wannan

Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki, Gwamnan PDP Ya Ƙara Jika Wa Zababɓen Gwamna Aiki

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa ta'addancin 'yan bindiga a arewacin Najeriya na nema ya dawo bayan sauƙin da aka samu a kakar zaɓe da sauya fasalin naira.

Gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa canja takardun kuɗi ya taimaka wajen raguwar ayyukan 'yan ta'adda a sassan ƙasar nan.

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dalibai Kusan 10 a Jihar Kaduna

A wani labarin kuma Yan bindiga Daji sun yi awon gaba ɗa ɗaliban wata makarantar Sakandire su kusan 10 a jihar Kaduna

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce a rahoton farko da gwamnatin Kaduna ta samu, an sace ɗaliban a karamar hukumar Kachia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262