An Gurfanar Da 'Yan Aikin Gida Gaban Kotun Kan Zargin Satar Zinare a Kano

An Gurfanar Da 'Yan Aikin Gida Gaban Kotun Kan Zargin Satar Zinare a Kano

  • Wasu ƴan aikin gidan da ake zargin su da satar zinaren maƙudan kudaɗe sun gurfana a gaban kotun musulunci
  • Ana tuhumar ƴan aikin gidan ne dai da laifin sace zinare a gidan da aka ɗauke su suna aiki a jihar Kano
  • Ƴan aikin sun ƙeƙasa ƙasa sun ce sam ba su san wannan zancen zargin satar da aka laƙa musu ba

Jihar Kano- An gurfanar da wasu ƴan aikin gida a gaban wata kotun shari'ar musulunci mai zaman ta a Kwana Hudu a jihar Kano, kan zargin aikata laifin sara.

Ana zargin ƴan aikin gidan da haɗa baki baki wajen sace zinare wanda kuɗin sa ya wuce naira miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu (N1.4m) daga gidan da suke aiki. Rahoton Daily Trust

Kotun
An Gurfanar Da 'Yan Aikin Gida Gaban Kotun Kan Zargin Satar Zinare a Kano Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Laifin na su ya saɓawa sashin doka na 120 da 133 na dokar shari'ar musulunci ra jihar Kano.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Badakalar Bacewar N20bn Daga Asusun NNPC

Wani mai suna Khalid Mahmud Badawa, shine ya shigar da ƴan aikin gidan masu suna Ketura Danjuma da Aisha Abdullahi, ƙara a gaban kotun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai shigar da ƙara, Aliyu Abidin Murtala, ya gayawa kotun cewa waɗanda ake zargin sun shiga cikin ɗakin matar wanda yake ƙarar ne, inda suka fake da cewa suna gyaran gidan ne sannan suka sace zinaren.

Sai dai, ƴan aikin gidan da ake zargi da laifin aikata wannan gagarumar satar sun musanta zargin da ake tuhumar su da shi.

Alƙalin kotun, mai shari'a Nura Yusuf Ibrahim, ya bayar da umurnin a tsare waɗanda ake zargin a gidan gyaran hali, sannan ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 10 ga watan Mayun 2023.

Kotun Musulunci Ta Yanke Wa Barawon Rake Hukunin Bulala 10 A Kano

A wani labarin na daban kuma, wata kotun shari'ar musulunci a jihar Kano ta zartar da hukuncin ta kan wani ɓarawon rake da aka gurfanar da shi a gaban ta.

Kotun ta bayar da umurnin a bulale wanda ake ƙarar saboda laifin satar da ya tafka a gonar raken ɗa ba tashi bace. Mai gonar raken dai shine ya shigar da ƙarar bayan ya cafke shi yana masa halin ɓera a cikin gonar sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng