Kashim Shettima Ya Yiwa 'Yan Achaba Wani Muhimmin Alkawari
- Zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya kwantarwa da ƴan achaɓa hankali
- Shettima yayi musu alƙawarin hana ƙwace musu babura da lalata su da akeyi a ƙasar nan
- Akwai wurare da dama inda aka hana achaɓa a ƙasar nan waɗanda idan aka kama masu yi ana yin ƙwace da lalatawa
Abuja- Zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, yayi alƙawarin hana ƙwacewa da lalata baburan ƴan achaɓa a birnin tarayya Abuja, da sauran yankunan ƙasar nan idan ya hau mulki.
Shettima, wanda ya bayyana hakan a wani taron da ƙungiyar masu babura da kekuna masu ƙafa uku ta ƙasa, ya buƙace su da su cigaba da bin doka da oda domin gwamnati mai kamawa a shirye take ta kyautata musu. Rahoton Daily Trust
Zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasaɓ yayi nuni da cewa ƴan achaɓa da masu adaidaita sahu (Keke Napep) wakilan al'umma ne sannan su kwantar da hankulan su domin gwamnati mai kamawa zata yi duk abinda ya dace domin ganin ta kare musu mutuncin su.
Ba Bashi: Ministan Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Alkawari Da Shugaba Buhari Ya Cikawa 'Yan Najeriya
A birnin tarayya Abuja dai, hukumar kula da babban birnin na tarayya, ta sha ƙwace babura da lalata su na waɗanda suka karya dokar yin achaɓa a wuraren da aka haramta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ko a kwann nan hukumar ta lalata babura 476 da ta ƙwace a birnin waɗanda suka saɓa wannan doka. Rahoton The Cable
Tun da farko, kodinetan Arewa ta tsakiya na ƙungiyar Progressives Ambassadors, Engr Badru Abdul Rafiu, yace sun zaɓi kada su zama ƴan kallo inda suka yanke shawarar zuwa ayi tafiyar gina ƙasa wacce Asiwaje Bola Tinubu da Kashim Shettima suka jagoranta.
Haka kuma, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Usman Gwoza, ya gayawa zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasar cewa suna fuskantar ƙalubalen ƙwace musu babura da lalata su da hukumomi suke yi.
Gwamnati Ta Gama Shirin Janye Tallafin Fetur, An Karbo $800m Daga Bankin Duniya
A wani labarin na daban kuma, gwamnatin Najeriya ta kammala shirin janye tallafin man fetur da take badawa, ta karɓo maƙudan kuɗi daga bankin duniya domin ragewa ƴan Najeriya raɗaɗi.
Gwamnatin ta karɓo $800m domin rabawa ga ƴan Najeriya.
Asali: Legit.ng