An Kama Malamin Makaranta Dumu-Dumi Yana Cika Tumbinsa Da Abincin Wata Daliba a Aji, Bidiyon Ya Yadu

An Kama Malamin Makaranta Dumu-Dumi Yana Cika Tumbinsa Da Abincin Wata Daliba a Aji, Bidiyon Ya Yadu

  • Bidiyon wani malamin makaranta yana cika tumbinsa da abincin daya daga cikin dalibansa a aji ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Mutumin ya cika cokali mai yatsu na yarinyar da taliya da ya debo daga kwanon abincinta sannan ya cika bakinsa da shi yayin da take kallo
  • Yayin da wasu masu amfani da soshiyal midiya suka nuna rashin jin dadinsu kan abun da malamin ya yi, wasu sun kare shi

Bidiyon wani mutum da ake zargin malamin makaranta ne ya yadu a soshiyal midiya bayan an hasko shi yana cin abincin daya daga cikin dalibansa a aji.

An wallafa bidiyon da ke nuna mutumin yana kwasar girkin a Instagram ne kuma ya haddasa cece-kuce a tsakanin mutane.

Malami yana cin abincin dalibarsa a aji
An Kama Malamin Makaranta Dumu-Dumi Yana Cika Tumbinsa Da Abincin Wata Daliba a Aji, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

Rike da lasifika a hannu daya, malamin ya duka sannan ya cika cokali mai yatsu da taliya da ya debo daga kwanon abincin yarinyar sannan ya sanya a bakinsa.

Kara karanta wannan

Portable Mai Wakar Zazoo Ya Garzaya Masallaci Kai Tsaye Don Yin Sallah Bayan Yan Sanda Sun Sako Shi, Bidiyon Ya Yi Farin Jini

Yarinyar na kallonsa yana ci mata abinci. Sai dai, ya tashi tsaye sannan ya cika da mamaki bayan ga cewa an kama shi dumu-dumu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng bata da tabbacin ko an shirya abun ne ko kuma da gaske ne a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@queen_vaughanta ce:

"Mutumin da bai iya gani ya kyale da kamun kai zai iya yin fiye da haka ba tare daan kama shi ba. Idan wannan ba wasan kwaikwayo bane, wannan dabi'ar ba abun yarda bane saboda sharhin da ke nan ya sa abun ya yi kamar dabi'a ce a makarantun Najeriya. Ina fatan wannan ne abu mafi muni da ya aikata saboda ni ban fahimta ba."

@officialdjsmart ta ce:

"Da lasifika a hannunsa da kuma yanayin shigar yaron da ke kusa da mai abincin, ina ganin MC ne na ranar al'ada a makarantarsu amma ba malami ba."

Kara karanta wannan

"Namijin Duniya": Bidiyon Yaro Dan Watanni 7 Yana ‘Dare Tsani Ya Bar Mutane Baki Bude

@chinurum_ ta ce:

"Wannan ya tuna min da malaminmu na aji 5 a Firamare...ana zagawa da kwanon abincinsa a aji don mu tattara masa abincinmu.
"Muna farin cikin yin hakan don me zai hana."

Matar Oba Elegushi ta tashi kan jama'a da abayar miliyan N2.9

A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a sun girgiza matuka a soshiyal midiya bayan cin karo da hoton matar basaraken kasar Yarbawa, Hadiza Elegushi sanye da wata abaya da farashinta ya kai miliyan N2.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel