An Tayar Da Jijiyar Wuya Yayin Da Jami'ar Babban Fasto Ta Hana Dalibai Musulmai Shiga Da Hijabi

An Tayar Da Jijiyar Wuya Yayin Da Jami'ar Babban Fasto Ta Hana Dalibai Musulmai Shiga Da Hijabi

  • Jami'ar Covenant ta fasto David Oyedepo ta hana ɗalibai musulmai mata shiga harabar ta da hijabi
  • An yi Allah wadai kan wannan hukuncin da jami'ar ta yanke na nuna wariya ga ɗaliban masu rubuta jarabawar gwaji ta JAMB
  • Hukumar JAMB ba tace uffan ba kan wannan rashin adalcin da aka nunawa ɗalibai musulmai a jami'ar

Jihar Ogun- Ana cigaba da Allah wadai kan hukuncin da shugabannin jami'ar Covenant University, ta babban fasto Bishop David Oyedepo shugaban cocin Living Faith Church Worldwide, na hana ɗalibai musulmai masu sanye da hijabi rubuta jarabawar gwaji ta JAMB.

Jami'ar ta Covenant ta dai hana ɗaliban zaunawa jarabawar ne a harabar ta dake Otta, jihar Ogun.

Covenant
An Tayar Da Jijiyar Wuya Yayin Da Jami'ar Babban Fasto Ta Hana Dalibai Musulmai Shiga Da Hijabi Hoto: Blackbox Nigeria
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an hana ɗaliban mata shiga cikin harabar makarantar ne saboda kawai suna sanye da hijabi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Shiga Cikin Jihar Kano, Sun Yi Garkuwa da Matar Wani Basarake da Ɗansa

A wani bidiyo mai tsawon 1:14 da wakilin jaridar yaci karo da shi, an nuna ɗalibai mata huɗu sanye da hijabi waɗanda aka hana shiga cikin jami'ar saboda kawai suna sanye da abinda ya kare musu mutuncin su. Rahoton Sahara Reporters

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mahaifi, Mr. Olayode Akeem, wanda ya raka yarinyar sa zuwa wajen jarabawar, yace masu gadi ɗalibai masu sanye da hijabi shiga cikin makarantar saboda suna bin umurnin da aka basu daga sama.

Sai da JAMB ta sanya baki sannan aka bar ɗaliban suka shiga cikin makarantar bayan sun kwashe fiye da sa'a ɗaya suna jira a waje.

Wani majiyar ganau ba jiyau ba wanda yake zama a Ota ya bayyana cewa:

“Naje jami'ar Convenant a ranar Juma'a kuma na ganewa idona aukuwar hakan. Wata budurwa an gaya mata cewa ba zata shiga ba ta rubuta jarabawar har sai ta cire hijabinta ko kuma ta mayar da ahi kallabi. Wannan cin zalin yayi yawa. Abin takaici ne sannan yakamata a magance sa kafin zuwan ranar jarabawar."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗaliban Wata Makaranta a Jihar Kaduna

Mutane da dama sun yi rubuce-rubuce a Twitter domin yin Allah wadai da abinda jami'ar tayi, inda suka yi kira ga hukumar JAMB da magance matsalar kafin zuwan ranar babbar jarabawar.

Haka kuma, ƙungiyoyin musulunci da dama sun yi Allah wadai da hakan a cikin sanarwar da suka fitar.

Ƙungiyoyin The Hijab Rights Advocacy Initiative (HRAI) da Muslim Rights Concern (MURIC), a cikin sanarwar da suka fitar daban-daban sun bayyana cewa wasu ɗaliban sai da suka cire hijaban su kafin aka kyale su suka shiga cikin makarantar.

Har yanzu dai hukumar JAMB ba tace komai game da halin ƙuncin da ɗalibai musulmai mata suka tsinci kan su ba a jami'ar Covenant.

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

A wani rahoton, tsohon sarkin masarautar Kano, Sanusi Lamido Sanusi II, ya bayyana manyan barzanar da ƙasar nan ke fuskanta.

Tsohon basaraken yace tun bayan yaƙin basasa ƙasar nan bata taɓa shiga irin wani mummunan yanayi ba kamar wanda take ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng