An Kama Mutumin da Ya Cire Kokon Kai 50 Daga Kaburbura a Wani Yankin Jihar Ogun
- An kama wani mutumin da ke shiga makabarta yana sace kokon kan mamatan da aka binne tare da yin tsafi dasu
- An sha jin labarin yadda ake sace kokon kan mamata a yankin da lamarin ya faru, shugabanni sun fara daukar mataki
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano bakin zaren kafin daga bisa a gurfanar dashi a gaban kotu
Jihar Ogun - Shugabannin yankin Ipokia a karamar hukumar Ipokua ta jihar Ogun sun kame wani mutun mai suna Gbesemehan Dewanu Solomon bisa zarginsa da tone karburbura a garin.
An ruwaito cewa, Solomon na tone kaburburan ne tare da cire kokon kawunan mamatan da aka binne, rahoton Vanguard.
Idan baku manta ba, rahotanni a baya sun bayyana cewa, an shiga wani hali na yadda ake yawan tone kaburbura a yankin Ipokia, ana zargin matsafa da yin hakan.
A baya-bayan nan, mazauna yankin sun ce akalla kokon kai 50 ne aka tone aka tafi dasu tare da zargin ana aikata tsafi ne da su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda aka kama mai tono kaburburan
Ba tare da dogaro da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba, shugabannin yankin sun tashi tsaye domin tabbatar da sun kubutar da yankinsu, inda suka kama mai aikata barnan.
An tattaro cewa, hakarsu ta kai ga ruwa yayin da suka kame Solomon a ranar Litinin a wani wuri da ake kira Idologun.
An gano cewa, wanda aka kamen yana kokarin tono wani kabari ne sai mutanen yankin suka yi ram dashi, Daily Post ta ruwaito.
Bayan kame shi, an gano jakarsa dauke da kayayyakin da yake amfani dasu wajen tono kaburbura tare da tafiya dasu.
Shugaban yankin, Oba Yisa Olaniyan ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni aka mika wanda aka kamen ga ‘yan sanda.
Ma’aikatan muhalli za su rufe makabarta a Abuja
A wani labarin kuma, ma’aikatan muhalli a Abuja sun yi barazanar yin yajin aiki tare da rufe makabartun birnin.
Wannan ya faru ne bayan da suka gabatar da bukatarsu ta aiki amma gwamnati ta gaza biya musu cikin lokacin da ya dace.
Ma’aikata a Najeriya na yawan shiga yajin aiki da zanga-zanga kan neman hakkinsu a hannun gwamnati.
Asali: Legit.ng