Bayan Shan Dogon Cece-Kuce a Kafar Sada Zumunta, Peter Obi Ya Yi Magana Kan Faifan Muryarsa da Ya Fito

Bayan Shan Dogon Cece-Kuce a Kafar Sada Zumunta, Peter Obi Ya Yi Magana Kan Faifan Muryarsa da Ya Fito

  • Bayan tonuwar asirinsa, Peter Obi ya sake yin magana game da matsayarsa kan Najeriya da makomarta
  • Obi ya ce, bai da shirin bata suna ko cin amanar kasar nan, don haka a daina yada jita-jita a kansa
  • A kwanakin baya wani faifan murya ya fito na yadda Obi ke neman a shawo kan kiristoci a Arewacin Najeriya

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi magana game da wani faifan murya da ya yadu na tonon sililin shirinsa tsakaninsa da Bishop David Oyedepo game da zaben shugaban kasa.

Faifan muryar da jaridar Gazette ta fitar ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta a ranar Asabar din da ta gabata.

A cikin faifan, an ji lokacin da Obi ke rokon gingimemen malamin na coci da ya shawo masa kan kiristoci a Arewa ta Tsakiya kan su kada masa kuri’u a zaben da ya gabata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Buhari Ta Zargi Peter Obi Da Cin Amanar Kasa

Peter Obi ya magantu kan batun cewa ya ci amanar kasa
Peter Obi da Lai Muhammad | Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Hakazalika, an ji Obi na cewa, zaben na bana batu ne na yaki tsakanin addinin kirista da Islama, don haka a shawo masa kan jihohin Kwara, Kogi da Neja da ke Arewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin Peter Obi game da cewa ya ci amanar kasa

Sai dai, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata 4 Afirilu, 2023 ya yi magana mai kama da martani game da faifan da ya yadu.

Hakazalika, a batun nasa, ya caccaki ministan yada labarai na Najeriya da ya zarge shi da cin amanar kasa bisa yin maganganu masu tada hankali.

A kalaman Obi:

“A kwanakin bayan nan, na lura ana yada cece-kuce mai muni game dani, ga kuma batun baya-bayan na ministan yada labarai, Lai Muhammad daga birin Washington DC.”

Ya yi Allah-wadai da batun ministan, inda yace sam ba shi da mugun nufi game da Najeriya ko kokarin bata sunata.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye

Bani da nufin bata suna ko cin amnara Najeriya, inji Obi

Ya kara da cewa:

“Ban taba magana ko karfafa gwiwar wani ya rana kasa Najeriya ba; ban taba daukar nauyi ko yin da’awar wani aiki game da kasa Najeriya ba.
“Wadanda ke faro irin wadannan ayyukan suna ci gaba da amfani da kujerunsu na gwamnati da wakilansu wajen shafa mani kashin kaji.”

Peter Obi ya yi magana bayan da asirinsa ya tono kan shirinsa na hada kai da kiristoci domin karbar mulkin Najeriya. Ya bayyana kadan daga abin da yake magana akai, inda yace bai da shirin bata Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.