Tashin Hankali Yayin Da Masu Zanga-Zanga Suka Dira Ofishin Hukumar INEC Da Kayan Bokaye a Rivers
- Masu zanga-zangar jam'iyyar PDP a jihar Rivers sun zo da sabon salo wajen zanga-zangar su
- Ƴaƴan jam'iyyar ta PDP sun dira a gaban ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar sanye da kayan bokaye
- Masu zanga-zangar na neman sai hukumar zaɓen ta INEC ta biya musu buƙatun su da suke nema
Jihar Rivers- An samu tashin hankali a wajen babbar kofar shiga ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta jihar Rivers, a safiyar ranar Talata, lokacin da masu zanga-zanga na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), suka cigaba da zanga-zangar su.
Masu zanga-zangar dai sun dawo wajen ne ɗauke da kayayyakin tsafi da kuma boka. Rahoton Leadership
Masu gudanar da zanga-zangar suna cikin rana ta biyu ta zanga-zangar ne, inda suke neman hukumar zaɓen ta bari a duba kayayyakin zaɓen jihar a tare da sauran masu son dubawa.
A ranar Litinin dai sun farmaki ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Tonye Cole, sannan suka hana shi shiga ofishin hukumar zaɓen inda ya shirya ganawa da wasu jami'an hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lokacin da aka cigaba da zanga-zangar a ranar Talata, shugaban ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar, Samuel Nwanosike, ya taho da shiga ta fararen kaya da farar hula inda ya dinga karanto kalaman tsubbu cikin yaren sa na Ikwerre.
Zanga-zangar ta yau Talata ta samu halartar mambobin majalisar dokokin jihar da dama waɗanda suka haɗa da kakakin majalisar Martins Amaewhule, da mataimakin sa Edison Ehie. Rahoton Channels Tv.
Suna zargin ɗan takarar APC
Bayan neman da suke na bari su a duba kayayyakin zaɓen jihar tare, suna kuma neman da aka cafke ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar bisa zargin kisan kai.
Suna zargin Cole da jagorantar ƴan daba domin kai musu farmaki lokacin zanga-zangar su a ranar Litinin, wanda ake zargin ran mutum ɗaya ya salwanta.
Sun bayyana cewa jam'iyyar tuni ta rubuta koken ta zuwa ga kwamishinan ƴan sandan jihar domin a cafke Tonye Cole da tuhumar sa.
Dan Takarar Gwamnan APC a Rivers Ya Koka
A wani rahoton ɗan takarar gwamnan APC a jihar Rivers ya koka tuggun da ake haɗa wa jam'iyyar sa a jihar.
Ɗan takarar yayi ƙorafin cewa ana shirya maƙarƙashiya domin hana shi zuwa kotu.
Asali: Legit.ng