Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dalibai Kusan 10 a Jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dalibai Kusan 10 a Jihar Kaduna

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki, sun yi awon gaba da ɗaliban wata makarantar Sakandire a karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar yau Talata
  • Ya ce a rahoton farko da hukumomin tsaro suka aike wa gwamnati, ba bu ainihin wurin da aka sace ɗaliban

Kaduna - Miyagun 'yan bindigan daji sun yi awon gaba da ɗalibai kusan 10 a yankin ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Gwamnatin Kaduna karkashin gwamna Malam Nasiru El-Rufai, ta ce ta samu rahoto daga hukumomin tsaro dangane da lamarin garkuwa da ɗalibai 10 a ƙaramar hukumar Kachia.

Harin yan bindiga a Kaduna.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dalibai Kusan 10 a Jihar Kaduna Hoto: vanguard
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust ya ce hakan na ƙunshe a wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ranar Talata 4 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Miyagun Yan Daba Sun Kusa Sheƙe Ɗan Takarar Gwamnan APC a 2023

A cewar rahoton farkon, Ɗaliban makarantar Sanadire da ke Awan (makarantar sakandiren jeka ka dawo) sun shiga hannun masu garkuwa da mutane ranar Litinin da ta gabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamishinan tsaron cikin gidan ya ce har yanzun ba'a gano taƙamaiman wurin da maharan suka sace ɗaliban Sakadiren ba.

Mista Aruwa ya ƙara da cewa har yanzun gwamnati na dakon cikakken rahoton yadda lamarin ya faru domin fayyace gaskiyar a cikin harabar makarantar lamarin ya afku ko a wani wuri daban.

Bugu da ƙari, kwamishinan ya yi alƙawarin cewa da zaran ya samu ƙarin bayani kan batun zai fitar da sanarwa a hukumance, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kaduna na cikin jihohin arewa maso yamma da ke fama da ta'addancin yan fashin daji da masu garkuwa da mutane. Zamfara, Katsina da Sakkwato duk matsalar ta taɓa su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sanya Dokar Kulle a Wani Yanki a Jihar

Bayan Sace Ɗalibai Mata 2, An Jibge Jami'an Tsaro a Jami'ar Tarayya Gusau

A jihar Zamfara kuma, bayan abinda ya far ranar Lahadi, jami'an tsaro sun ƙara tsaurara tsaro a gidajen kwanan ɗaliban jami'ar tarayya Gusau

Wannan ya biyo bayan harin da wasu yan fashin daji suka kai, inda suka yi awon gaba da ɗalibai mata biyu ranar Lahadi da ta gabata.

Sai dai ɗaliban sun tsorata sun bar gidajen kwanansu, amma bayan zuwan dakarun tsaro sun fara komawa gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262