IGP Ya Gana da Sabon Shugaban Hukumar PSC, Ya Faɗi Abinda Suka Tattauna

IGP Ya Gana da Sabon Shugaban Hukumar PSC, Ya Faɗi Abinda Suka Tattauna

  • IGP Usman Alkali Baba, ya gana da sabon shugaban hukumar kula da ayyukan yan sanda ta ƙasa, Solomon Arase, tsohon sufeta janar
  • Manyan shugabannin biyu sun gana da juna a ɗakin taron da ke Sakatariyar hukumar PSC da ke Abuja ranar Litinin 3 ga watan Afrilu
  • Bayan fitowa taron, IGP Baba ya gaya wa yan jarida manyan batutuwan da suka sa ya kai ziyara ga Arase

Abuja - Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan ƙasar nan, Usman Alƙali Baba, ya gana da sabon shugaban hukumar jin daɗin 'yan sanda (PSC), Solomon Arase, tsohon IGP.

Punch ta rahoto cewa ɓangarorin biyu sun gana da juna a ɗakin taron PSC a Sakatariyar hukumar ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin 3 ga watan Afrilu.

IGP ya gana da Arase.
IGP Ya Gana da Sabon Shugaban Hukumar PSC Hoto: Punchng
Asali: UGC

A zamansu, sun yi kokarin lalubo hanyar ƙara ɗankon kyakkyawar alaƙa tsakanin rundunar yan sanda (NPF) da hukumar kula da ayyukansu (PSC).

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Kulla-Kular Da 'Yan Siyasa Ke Yi Domin Samun Shugabancin Majalisa

Haka zalika manyan shugabannin hukumomin guda biyu sun tattauna yadda za'a ƙara karfin zumunci da aiki kafaɗa da kafaɗa a tsakanin NPF da PSC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

IGP ya faɗi dalilin da ya sa ya gana da Arase

Da yake hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan taron, shugaban 'yan sanda, IGP Baba ya ce ya kai wannan ziyara ne domin kara inganta alaƙar 'yan sanda da PSC da kuma shawo kan matsalar tsaro a ƙasar nan.

IGP, wanda ya ta ya sabon shugaban PSC murnar fara aiki, ya ce:

"Na kawo ziyara hukumar PSC ne domin na ta ya murnar fara aikin sabon shugabam hukumar, Solomon Arase (Sufeta janar mai ritaya)."
"Da zaran an samu ingantacciyar alaƙa, jagoranci na gari, nuna hanya, hukunci, ƙarin girma, naɗe-naɗe, to mutane zasu samu karsashin aikata abinda yake daidai."

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Buhari, Sabon Gwamna Ya Bayyana Sabuwar Hanyar Yaƙi da 'Yan Bindiga

An kafa kwamitin da zai magance kalubalen ɗaukar aiki

Leadership ta rahoto cewa hukumar PSC da rundunar yan sanda sun kafa kwamiti, wanda ya ƙunshi mambobi daga kowane bangare, da nufin kawo ƙarshe rikicin ɗaukar sabbin yan sanda.

Shugaban PSC, Solomon Arae, ne ya bayyana haka bayan ya karɓi bakuncin IGP a Abuja. Ya ce kwamitin zai lalubo hanyar kawo karshen rikicin ɗaukar ma'aikata wanda NPF da PSC zasu amince.

A wani labarin kuma An bayyana Babban Tasirin da Canjin Kuɗi Ya Yi Kan 'Yan Bindiga, Masu Garkuwa da Yan Siyasa

Ministan Kwadugo, Dakta Chris Ngige, ya bayyana babban ci gaɓan da saura fasalin naira ya kawo a rayuwar talakawan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262