Mutum 1 Ya Jikkata Yayin da Magoya Bayan PDP da APC Suka Yi Kaure da Fada a Ribas

Mutum 1 Ya Jikkata Yayin da Magoya Bayan PDP da APC Suka Yi Kaure da Fada a Ribas

  • An samu hargitsi tsakanin 'yan APC da PDP a lokacin da suke zanga-zanga kan batun da ya shafi sakamakon zabe
  • An harbi wani dan a mutun PDP a lokacin da yake kokarin tunkarar jami'in tsaron da ke tare da dan takarar gwamnan APC
  • Ya zuwa yanzu, babu wasu cikakkun bayanai da ke nuna yadda aka shawo kan lamarin da kuma halin da mai rauni ke ciki

Jihar Ribas - Wani mutum ya samu mummunan raunin harbin bindiga a lokacin da magoya bayan jam’iyyar APC da PDP suka kaure da fada a Fatakwal ta jihar Ribas a ranar Litinin.

A tun farko, wasu magoya bayan PDP sun yi zanga-zanga a gaban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta da ke hanyar Aba a birnin na Fatakwal.

Masu zanga-zangar na neman a yi zaman gaba-gadi don duba tare da bincike kan kayayyakin aikin zabe da dukkan jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Rantsar da Sabon Shugaban Kasa, Wata Jam’iyya Ta Kai Tinubu Kotu

Yadda rikicin APC da PDP ya kai ga harbin wani a Ribas
Jihar Ribas ta PDP, jihar Wike | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

APC za ta dumfari ofishin INEC

Jam’iyyar APC, karkashin jagorancin dan takararta na gwamna a jihar, Tonye Cole a ranar Juma’ar da ta gabata ta ce za ta fito don mika kokenta a ofishin hukumar zabe ta INEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Cole, za a mamaye ofishin na INEC ne domin tabbatar da an saki sahihan takardun aikin zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris don ba APC damar shigar da karar kalubalantar zaben.

Dan jaridar Punch da ke wurin da kitimurmurar ke faruwa ya ce, yayin da ‘yan PDP ke zanga-zanga, Cole da shugaban APC na jihar, Emeka Beke da sauran ‘yan APC sun bayyana a ofishin na INEC.

Matasan da ke zanga-zanga sun dumfari inda suke, inda suka yi ta jifan Cole da ‘yan tawgaarsa ta 'yan APC.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Jerin jiga-jigan siyasan APC 3 da ke son maye gurbin Yahaya Bello da tasirinsu

Yadda aka tafi da Cole, 'yan PDP na jifa

Wasu jami’an tsaron da ke tare da Cole sun tafi dashi a mota, inda ‘yan zanga-zangar PDP suka ci gaba da jifa da ledojin ruwa da duwatsu, Within Nigeria ta ruwaito.

Cikin kankanin lokaci, sojojin 6 Division, ‘yan sanda da jami’an NSCDC suka iso wurin tare da fara harbin iska don watsa masu zanga-zangar.

Sai dai, wani ganau ya shaida cewa, wani jami’in tsaro da ke tare da Cole ya harbi wani daga cikin masu zanga-zangar da ya yi ta kansa.

An ruwaito cewa, ya samu mummunan raunin da yasa ya kwanta a kasa kafin daga bisani abokansa suka dauke shi.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu wani bayani na yadda aka shawo kan lamarin ba da kuma halin da wanda ya samu raunin ke ciki.

A yanayi irin wannan, APC da NNPP ke musayar miyau kan lamarin da ya shafi zaben gwamna na wannan shekarar.

Kara karanta wannan

To fah: INEC ta yi hayar wasu manya, fitattun lauyoyi 9 a Najeriya don kare sakamakon zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.