An Gurfanar Da Shahararren Mawaki Portable a Gaban Kotun Majistare

An Gurfanar Da Shahararren Mawaki Portable a Gaban Kotun Majistare

  • Ƙarshen alawa ƙasa, mawaƙin nan Portable ya gurfana a gaban kotu bayan ƴan sanda sun yi caraf da shi
  • Rigimammen mawaƙin ya saba taƙun saƙa da ƴan sanda inda a baya ya ƙi yarda da su cafke shi
  • Mawaƙin yana fuskatantar tuhumomi da dama a gaban kotu waɗanda ake zargin sa da aikatawa

Jihar Ogun- Rigimammen mawaƙin nan, mai suna Habeeb Okikiola wansa aka fi sani da Portable, ya gurfana a gaban kotun majistare ta Ifo a ƙaramar hukumar Ogun. Rahoton The Cable

Tun da farko rundunar ƴan sandan Najeriya (NPF) ta bayyana cewa Portable zai fuskanci tuhumomi fiye da 6 bisa zargin duka a gaban kotu.

Portable
An Gurfanar Da Shahararren Mawaki Portable a Gaban Kotun Majistare Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ta bayyana cewa tuni aka gurfanar da mawaƙin a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano Tayi Babban Kamu, Ta Cafke Wasu Miyagun Bata Gari Da Suka Addabi Jihar

“Yana kotu. Yanzu haka yana cikin kotu. An gurfanar da shi." A cewar ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar juma'a ne dai akayi caraf da Portable bayan wa'adin sa'o'i bakwai da ƴan sanda suka ba shi ya kawo kansa gare su.

Mawaƙin dai ya fara shiga taƙun saƙa da ƴan sanda ne ranar da ta gabata bayan ya ƙi yarda ƴan sanda su kama shi a jihar Ogun.

Mawaƙin ya haƙiƙance cewa babu wani dalilin kama shi inda ya ƙara da cewa yana samun kuɗaɗen sa ne ta halastacciyar hanya.

Mawaƙin mai shekara 29 ya kuma kira kan sa a matsayin kadarar gwamnatin tarayya.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Muyiwa Adejobi, yace za a gurfanar da Portable ne bisa laifin yin duka, da kuma ƙin yarda a kama shi da raunata jami'in ɗan sanda. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

"Za a gurfanar da shi a kotu bisa yiwa wani matashi dukan tsiya wanda ya shigar da ƙara a gaban kwamishinan ƴan sandan jihar Ogun." Adejobi ya rubuta a Twitter.

Badakalar N40m: Jarumar Kannywood, Amal Umar Ta Roki Kotu Da Ta Hana Yan Sanda Kama Ta

A wani labarin na daban kuma, shahararriyar jarumar masana'antar finafinai ta Kannywood ta garzaya gaban kotu ɗauke da ƙoƙon baran ta.

Jaruma Amal Umar na neman kotu ta hana ƴan sanda yin ram da ita saboda baɗaƙalar wasu maƙudan kuɗaɗe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng