“Kin Huta da Biyan Haya”: Jama’a Sun Taya Budurwar da Ta Gida a Bakin Hanya Mai Kama da Bandaki

“Kin Huta da Biyan Haya”: Jama’a Sun Taya Budurwar da Ta Gida a Bakin Hanya Mai Kama da Bandaki

  • Wata budurwa ta yi tunani, ta yi amfani da ‘yan kudadenta wajen gina dan karamin gida don huce biyan kudin haya duk shekara
  • Da take yada bidiyon gida, ta ce duk da cewa gidan karami ne, amma tana jin dadin ta mallaki muhallinta
  • ‘Yan TikTok ba a barsu a baya ba, sun yi martanin yaba mata da samun wannan nasara na gina gida

Wata budurwa, @kakokaondjafa ta yada wani bidiyo mai daukar hankali na dan karamin gidan da ta yi nasarar ginawa kanta.

A cewarta, tana jin dadin a yanzu ita ma ta mallaki gida nata na kanta duk kuwa da ya yi daban da irin gidajen da aka saba gani.

Gidan nata dai wani dan karami ne kamar rumfar ‘yan sanda a bakin titi, amma a haka ta zuba masa tayel masu kyau.

Kara karanta wannan

“Ki Je Ki Gwada a Bariki”: Budurwa Ta Kwace Waya Daga Hannun Soja, Bidiyon Ya Yadu

Budurwa ta gina karamin gida mai ban mamaki
Hotunan gidan da budurwa ta ginawa kanta | Hoto: @kakokaondjafa
Asali: TikTok

Gidan nata mai daki daya ne, don haka ta shimfida gadonta a ciki, ga kuma karamar tagar shan iska ta gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mashigar gidan kuwa, wata kofa ce aka yi ta da katako. A wani bidiyon na daban, an ga tana yiwa cikin dakin fenti.

Jama’ar kafar sada zumunta dai basu yi shuru ba, sun yi martani da tofin albarka game da wannan nasara da ta samu na huta biyan kudin haya duk shekara.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akalla mutane 400 ne suka yi martani tare da dangwale sama da 15 kan bidiyon. Ga kadan daga martanin:

@BIG MERCY:

"Akalla dai ba za ki biya kudin haya ba, hakan ya yi kyau.”

@Cameroon football coach:

"Ina matukar alfahari dake ‘yar uwa. Allah ya kara budi amma ta yaya zan sauke bidiyon?”

Kara karanta wannan

Kaico: An debi 'yan kallo yayin da saurayi ya kama budurwa a otal tana karuwanci

@Glo_sante:

"Ki gwada yin tsakar gida, akalla za ki iya girki a ciki.”

@Stesh icequeen:

"Zan yi irin wannan a malindi nagode da ba ni shawari.”

@incognito:

"Babu wurin bahaya da wanka?”

@nebynedy76:

"Ina taya ki murna. Kada ki raina farawa da kadan-kadan.”

@ZAWADI TINA:

"Kin fi mu a yanzu da muke biyan kudin haya, ka biya kudin haya baka siya abinci ba. HAKAN YA YI KYAU SOSAI.”

@cissy321:

"Ban san yaushe zan ce wannan ne gida na ba.”

@ohenebaagyeman:

"Don Allah ki zagaye shi da katanga kada wasu su shiga su zaci bandaki ne.”

@seuntosin28:

"Ina taya ki murna ‘yar uwa akalla dai kin mallaki gida.”

@user7980821616629:

"Ina taya ki murna, babu abin da zai zama ya yi kadan a ginin gida.”

Wani bidiyo kuwa, ya nuna lokacin da maciji ke shiga wani bandaki don neman inda zai buya, jama'a sun shiga mamaki.

Kara karanta wannan

Iyali Sun Yi Amfani Da Tukunya a Matsayin Akwatin Daukar Gawa Don Bikin Mutuwar Kakarsu, Bidiyon Ya Bar Mutane Baki Bude

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.