Masu PoS Sun Zaftare Kudin Da Suke Amsa Yayin Da Aka Samu Wadatuwar Kudi

Masu PoS Sun Zaftare Kudin Da Suke Amsa Yayin Da Aka Samu Wadatuwar Kudi

  • Masu sana'ar (PoS) sun zaftare kuɗin da suke karɓa domin yin daidai da wanda babban bankin Najeriya (CBN) ya aminve da shi
  • Ƴan Najeriya da dama sun bayyana cewa yanzu masu Pos sun koma amsar kaso 5% na abinda zasu cira
  • Hakan na zuwa ne bayan gargaɗin da CBN yayi kan masu sana'ar masu tsawwala kuɗi ko siyar da naira

Samun isassun takardun kuɗin da aka fara yi ya sanya masu sana'ar (PoS) dole sun zaftare kuɗin da suke karɓa ya zuwa kusa da wanda babban bankin Najeriya (CBN) ya amince da shi kafin matsalar ƙarancin kuɗi.

BusinessDay ta rahoto cewa babban bankin CBN ya tabbatar da sakin takardun kuɗi daga rassanta zuwa ga bankuna a faɗin ƙasar nan, a ƙoƙarin da bankin yake domin rage matsalar ƙarancin kuɗi.

Kara karanta wannan

Mutane Da Dama Masu Azumin Jiran Haɗuwa Da Yesu Sun Kwanta Dama

Masu PoS
Masu PoS Sun Zaftare Kudin Da Suke Amsa Yayin Da Aka Samu Wadatuwar Kudi Hoto: Tina Hann
Asali: UGC

Ƴan Najeriya masu zuwa cirar kuɗi a PoS sun bayyana cewa a cikin ƴan kwanakinnan ana cajin su kusan abinda CBN ya amince a caja kafin sauya fasalin kuɗin ya sanya abinda ake cajar su yayi tashin gwauron zabo.

A cewar su, sun yi mamaki matuƙa da suka yadda abinda aka cajar yayo ƙasar warwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa suna biyan N500 kan kowacce N5,000 sannan suna biyan N1000 kan kowacce N10,000.

Tun lokacin da aka fara shiga matsalar ƙarancin kuɗi a watan Fabrairun wannan shekarar, ƴan Najeriya sun dogara ne akan masu PoS domin samun kuɗi a dalilin dogon layin da ake yi a injin cirar kuɗi (ATM) da kuma ƙayyade abinda za a iya cira da CBN ya ƙaƙaba.

Babban bankin na CBN ya sha a lokuta da dama faɗin cewa kaso 2% ne abinda masu PoS zasu riƙa cira akan kowane kuɗi da aka zo cira, sannan zai hukunta duk wani da ya saɓawa hakan.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Boye Kudin Su: Bankuna Sun Koma Ci Yo Bashin Biliyoyin Naira Wajen CBN

A lokacin da matsalar ƙarancin kuɗin tayi ƙamari sosai, masu PoS har abinda ya kai kaso 30% suna karɓa.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu wasu mutane a jihar Katsina kan sauyin da aka samu a dalilin fara yalwatuwar takardun kuɗi da aka samu.

Da yawa sun tabbatar da cewa masu POS sun rage kuɗin da suke caja idan aka je cirar kuɗi a wajen su.

Wani mai suna Zaharaddeen ya bayyana cewa:

"Eh yanzu gaskiya sun rage kuɗin da suke amsa, kuma yanzu ana samun kuɗi ba kamar kwanakin baya ba."

Wani mai sana'ar POS mai suna Abba ya bayyana cewa:

"Eh yanzu mun rage kuɗin da mu ke karɓa. Duk N1000 muna amsar N20 ko N30. Ko a baya lokacin da ƙarancin kuɗin yayi tsauri abinda mu ke amsa bai taɓa wuce N50 akan kowace N1000 ba."

Hukumar EFCC Ta Kama Masu Sayar POS 80 da Ke Siyar da Takardun Naira a Jihar Ondo

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari a Watan Azumi, Sun Kashe Mutane a Arewa

A wani labarin na daban kuma, wasu masu sana'ar PoS sun shiga hannun jami'an hukumar hana cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) a jihar Ondo.

Hukumar tayi caraf da su ne bisa yadda suke tsawwalawa mutane wajen cirar kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng