Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7, Sun Yi Garkuwa Da Wasu 26 a Jihar Neja

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7, Sun Yi Garkuwa Da Wasu 26 a Jihar Neja

  • Yan bindiga sun kai sabon hari kan al’umma a garuruwan Neja, sun kashe akalla mutane 7
  • Maharan da suka yi wa karamar hukumar Mashegun tsinke sun kuma yi garkuwa da mutane masu yawan gaske
  • Ciyaman din karamar hukumar Mashegu ya tabbatar da lamarin inda ya yi kira ga gwamnati da ta kawo agaji

Niger - Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutum bakwai sannan suka yi garkuwa da wasu 26 a garuruwa bakwai da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja.

Sabon harin yan ta'addan wanda ya ci tura cikin kwanaki biyar da suka gabata, ya raba mutanen garuruwan da abun ya shafa da gidajensu. Sun bar garuruwansu zuwa Kontagora, jaridar The Nation ta rahoto.

Taswirar jihar Neja da ke arewa ta tsakiya
Yan Bindiga Sun Hakala Mutum 7, Sun Yi Garkuwa Da Wasu 26 a Jihar Neja Hoto: Punch
Asali: UGC

Shugaban karamar hukumar Mashegun ya yi martani

Shugaban karamar hukumar Mashegun, Hon Umar Jibrin Igede, wanda ya tabbatar da hare-haren ga manema labarai ya koka kan lamarin.

Kara karanta wannan

Mutum 5 Sun Rasu A Hadarin Jirgin Ruwa A Kano, An Ceto Wasu Shida Da Ransu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce an kashe tare da sace daruruwan mazauna garuruwa bakwai da abun ya shafa daga watan Janairu zuwa Maris din 2023.

Igede ya ce:

"Tuni bakwai daga cikin garuruwan da ke karamar hukumar suka zama tamkar kufai sakamakon hare-haren rashin hankali da yan bindigar ke kaiwa.
"A cikin makonni biyu da suka gabata, yan ta'addan sun kai mummunan hari Kulhom Sahon Rami da Tashan Hajiya da sauran garuruwa. Yawancin mazauna kauyukan da abun ya shafa sun bar gidajensu zuwa sansanin gudun hijira a Kontagora da sauran wurare don samun mafaka."

Ya roki gwamnatin jihar da sauran hukumomin tsaro da su kawo masu dauki da kawo karshen harae-haren yan bindiga a yankin, rahoton Daily Post.

Legit.ng ta tuntubi wata mazauniyar yankin da ta nemi a sakaya sunanta inda ta ce sun shiga tashin hankali. Ta kuma ce tuni suka yi kaura zuwa garin Minna wajen danginsu domin samun mafaka.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Buhari Ya Fadi Lokacin Da Yan Najeriya Da Ke Zaune a Sudan Za Su Fara Dawowa Kasar

Ta ce:

“Wallahi hankalinmu ya tashi sosai, ni na kasa samun sukuni duk da cewar abubuwan sun lafa wannan dalilin ne ma ya sa na bukaci mai gidana ya barmu mu koma wajen yan uwanmu da ke Minna. Allah dai ya kawo mana saukin wannan al’amari.”

Yan bindiga sun farmaki dakin kwanan dalibai mata a Zamfara, an sace mutum 2

A wani labarin kuma, mun ji cewa mahara da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da dalibai mata biyu na jami’ar tarayya da ke Gusau (FUGUS) a jihar Zamfara.

An tattaro cewa al'amarin ya afku ne da safiyar ranar Lahadi, 2 ga watan Afirilu, lokacin da ‘yan ta’addan suka farmaki dakin kwanan daliban da ke Sabon-Gida.

Sabon-Gida dai wani kauye ne da ke kusa da babban kofar jami’ar, kuma ‘yan ta’addan sun daure masu gadin gidan daliban kafin suka sace su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng