Kotu Ta Yanke Wa Mutum 3 Hukuncin Rataya Saboda Kisa A Jigawa
- Wata babbar kotu da ke zamanta a Kaugama ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutane uku bisa zargin hada kai don aikata laifi, kisan kai da kuma fashi da makami
- Alkalin kotun ya kuma wanke daya daga cikin wanda ake kara bisa rashin gabatar da kwararan hujjoji da ke tabbatar da zargin da ake yi
- Wata kotun daban, ta yanke hukuncin daurin shekara 10 ga wani mutum bisa zargin yaudarar yaro dan shekara 11 ya ci zarafinsa
Jigawa - Wata babbar kotu da ke zamanta a Kaugama, da ke Jihar Jigawa, ta yankewa Sulaiman Bello, Auwalu Muhammed da Yakubu Muhammed kisa ta hanyar rataya bayan samun da hannu a tuhuma tara da suka hada da hadin kai don aikata laifi, kisan ganganci da kuma fashi da makami.
'Matsalolin' Najeriya Na Hana Ni Barci, Har Na Kamu Da Rashin Lafiya, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman
Ana zargin wanda ake kara da kashe wani Audu Saje na kauyen Manda a karamar hukumar Kaugama da ke jihar tare da guduwa da babur din shi, Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sun kuma yi garkuwa da wata Hadiza Abdullahi a garin Marma da ke karamar hukumar Kirikasamma tare da neman kudin fasan Naira miliyan 150.
Da aka binkica maboyarsu, bindiga AK-47 uku, GPMG daya; akwatin harsashi tara; harsashi 309; kudi kimanin Naira miliyan 2,070,000 da babur mallakin marigayi Audu Saje na cikin abubuwan da aka samu a wajen wanda ake kara.
Alkalin kotun, mai shari'a M. M Kaugama, da ya ke zartar da hukunci ya ce shari'ar karkashin jagorancin alkalin alkalan Jihar Jigawa, Dakta Musa Adamu, ta yi nasarar tabbatar da laifukan wanda ake kara na farko, na uku da na hudu (Suleiman Bello, Auwalu Muhammed da Yakubu Muhammed).
An gabatarwa kotu shaidu biyar
Kotun ta kuma ce, an kasa gabatar da gamsasshiyar hujja da ke tabbatar da laifin garkuwa da sata kan wanda ake kara.
Saboda haka, kotu ta sallami tare da wanke wanda ake kara na biyu Ya'u Mai Hatsi daga duk zargin.
An yanke wa wani hukunci kan cin zarafi
A wata shari'ar, babban kotu mai lamba 3 karkashin jagorancin mai shari'a M. A Sambo, ta yankewa Mustapha Isa na unguwar Auramo, da ke karamar hukumar Ringim a Jigawa daurin shekara 10 bisa laifin cin zarafi.
An zargi wanda ake kara da yaudarar yaro dan shekara 11 tare da cin zarafinsa cikin wani shago.
Da ake tuhumarsa, wanda ake karar ya musanta zargin.
A kokarin tabbatar da laifin wanda ake karar, kotu ta gayyaci shaidu biyar sun kuma gabatar da hujjoji hudu.
Daga ciki akwai rahoton asibiti da takardar tabbatar da laifin.
A karshen shari'ar, wanda ake karar ya fara kare kansa ya kuma bayyana kansa a matsayin DW1 ya kuma kira shaida daya a matsayin DW2 ya kuma kare daga nan.
Da ya ke zartar da hukuncin, mai shari'a A M Sambo ya ce lauyan mai kara, Kabiru Abdullahi, ya tabbatar da zargin da ake ba tare da kokwanto ba.
Asali: Legit.ng