Bidiyon Yadda Katon Maciji Ke Neman Mafaka a Bandaki Ya Ba Jama’a Mamaki

Bidiyon Yadda Katon Maciji Ke Neman Mafaka a Bandaki Ya Ba Jama’a Mamaki

  • Wani bidiyo a TikTok na wani katon maciji a cikin wani gida ya ba jama’a tsoro ganin yadda yake motsi
  • Bidiyon ya nuna lokacin da macijin ke neman wurin buya a gidan mutumin, lamarin da yasa mutane ke ta jin tsoro
  • Jama’a da yawa ne suka yi martani da ganin bidiyon, inda suke mamakin yadda ya samu wurin shan iska a gidan mutane

Jama’ar kafar sada zumunta da yawa ne suka bayyana mamaki da ganin katon maciji na neman wurin buya a bandakin wani gida.

Bidiyon ya samu martani da dangwale daga mutane da yawa da suka tsorata a kafar sada zumunta. Bidiyon dai ya sanya mutane da yawa jin tsoro matuka.

Bidiyon da @appel74 ya yada a TikTok ya nuna yadda katon macijin ke shiga wurin bahaya a bandaki, babban abin da ya ba jama’a mamaki shine yadda ya iya shiga ciki duk da girmansa.

Kara karanta wannan

Kaico: An debi 'yan kallo yayin da saurayi ya kama budurwa a otal tana karuwanci

Yadda maciji ya shige bandaki
Maciji sadda yake shiga bandaki | Hoto:@appel74
Asali: TikTok

Martanin jama’a game da bidiyon

Ba wannan ne karon farko na ganin bidiyon maciji a bandaki ba, hakan ya sha faruwa a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Irin wadannan dabbobin kan ba mutane mamaki. Wasu kan ce na tsoron amfani da bandakinsu bayan ganin bidiyo irin wannan.

Kalli bidiyon:

@leethehumble:

"Meye na kawo irin wannan? Zan koma amfani da gefen gado daga yanzu gaskiya.”

@smurfxttx:

"Kai, ba zan shiga bandaki ba bayan ganin wannan.”

@mdmtinisaleh:

"Yana bani tsoro irin wannan duk lokacin da na zauna a bandaki, sai fitsari kawai.”

@annmarie0745:

"Nakan duba nawa da kyau kafin na yi amfani dashi. Ina tsoron maciji.”

@dymondjohnson06:

"Ina ya shige? Har na fara jin tsoro a lokacin da na shiga bandaki. Wannan ya kara abin.”

@malindy70:

"Sadda nake kallon bidiyon nan a bandaki nake. Tashi na yi da gudu.”

Kara karanta wannan

“Duk Naki Ne Uwata”: Matashi Ya Kerawa Mahaifiyarsa Hadadden Gida, Bidiyon Ya Dauki Hankali

Yadda wani ya yi kiwon zaki na tsawon shekaru 11

A wani labarin kuma, wani mutum ya yi kiwon zaki na tsawon shekaru 11, ya bayyana hotunansa tare da dabbar mai ban tsoro.

Mutanen kafar sada zumunta sun yi martani, inda suka ce wannan lamari ne mai daukar hankali matukar da gaske.

Ba sabon abu bane a ga mutane na mu’alantar dabbobi masu hadari, musamman irin zakuna da ke rayuwa a daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.