'Yan Sanda Sun Hallaka ’Yan Ta’addan IPOB 5 a Jihar Abia da Kudancin Najeriya

'Yan Sanda Sun Hallaka ’Yan Ta’addan IPOB 5 a Jihar Abia da Kudancin Najeriya

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta tabbatar da cewa, ta sheke wasu ‘yan ta’addan IPOB biyar a lokacin da suka farmaki jami’ai
  • Rahoto ya bayyana cewa, wani ganau ya ce ‘yan ta’addan sun fito yin zanga-zanga ne amma ‘yan sanda suka hallaka su
  • Ana yawan samun farmakin ‘yan ta’addan IPOB a yankunan jihohin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a Najeriya

Jihar Abia - ‘Yan sandan jihar Abia sun bayyana cewa, a wani farmakin da ‘yan ta’addan IPOB suka kai kan jami’ansu, sune sheke tsagerun na IPOB biyar, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ikrari na ‘yan sanda na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Geoffrey Ogbonna ya fitar a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Mustapha Bala.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, an harbe ‘yan ta’addan na IPOB biyar ne a yankin Osusu Aba ranar Juma’a a lokacin da suke barna.

Kara karanta wannan

Sun Ji Wuta: Yan Ta'adda Sun Kashi Kashinsu a Hannu Yayin da Suka Kai Hari, An Kashe Su Da Dama

Yadda 'yan sanda suka sheke 'yan IPOB a Abia
Jihar Abia da ke Kudancin Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

‘Yan IPOB na zanga-zangar zaman lafiya, inji wani ganau

Wasu mazauna yankin da ke da bidiyon yadda lamarin ya faru sun ce, ‘yan ta’addan na IPOB na yin zanga-zangar lumana ne ba tare da hantarar kowa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mr Chinomso Aka, wani ganau ya ce, ‘yan ta’addan suna yin zanga-zanga ne game da ci gaba da tsare shugabansu Nnamdi Kanu, Punch ta ruwaito.

‘Yan IPOB sun fito dauke da makamai, inji ‘yan sanda

Sai dai sanarwar ‘yan sanda ta ce:

“Suna dauke da makamai da bama-baman fetur, adduna, gatura da sauran munanan makamai.
“’Yan sanda sun dakile harin tare da samun raunuka kanan yayin da da yawan ‘yan ta’addan suka tsere don tsira.
“Sai dai, komai ya koma daidai a yankin.”

Za mu tabbatar da zaman lafiya a Abia, inji ‘yan sanda

Kara karanta wannan

Jifan 'yan sanda: An kama daliban Zakzaky da yawa a wurin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba

A bangare guda, ‘yan sandan sun gargadi jama’ar gari, inda suka ce duk wasu masu kokarin kawo tsaiko ga zaman lafiya ba za su tsira ba , kuma su sake tunani kafin tunkarar ‘yan jami’an tsaro.

Hakazalika, rundunar ta ce jami’anta ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma yakar ‘yan ta’adda a jihar.

A wani labarin na daban, an kame wani basarake a jihar Imo bayan da aka zargi ya yada wasu kalamai masu zafi game da gwamnan jihar, Hope Uzodinma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.