“5 a Lokaci Daya”: Matashiya Ta Haifi Yan 5, Maza 3 Da Mata 2
- Wata matashiya yar Najeriya wacce ta gama yi wa kasa hidima kwannan nan ta haifi yara biyar a lokaci daya
- Matashiyar mai suna Chidimma Amaechi ta haifi yaran a Awka, babban birnin jihar Anambra
- Bayanan Facebook sun suna cewa matar ta shafe tsawon shekaru takwas ba tare da Allah ya bata haihuwa ba kafin wannan abun farin ciki da ya same ta
Wata matashiya yar Najeriya wacce ta yi wa kasa hidima kwanan nan ta samu karuwar yara yan biyar.
Matar mai suna Chidimma Amaechi wacce ta fito daga jihar Ebonyi ta haifi yaran a Awka, babban birnin jihar Anambra.
A bisa wani labari da Okoye Ifeoma Obi, ya wallafa a Facebook, mai jegon ta haifi yaran shinkafa da wake wato maza uku da mata biyu.
Wannan gagarumin ni'ima da Chidimma ta samu yana zuwa ne bayan ta shafe shekaru takwas ba tare da haihuwa ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani bangare na labarin ya ce:
"Mata na da karfi faaaaa. Yara biyar a lokaci daya. Ina rokon irin wannan, biyu kawai nake so. Wannan labari ne mai dadi da ya fito daga jihar Anambra. Ina taya Chidimma Amaechi wacce ta haifi yan biyar a Awka murnar wannan ni'ima na Ubangiji. Ta haifi maza 3 da mata 2 a asibitin Life Hospital Awka, jihar Anambra. Wannan ya cancanci ayi biki."
Kalli bidiyon a kasa:
Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi don taya matar murna.
Jama'a sun yi martani
Favour Chinedu ta ce:
"Ina tayaki murna yar'uwa, ina rokon Allah ya yi mun irin wannan abun farin cikin. Amin."
Oby Arikpo ta yi martani:
“Ka Duba Darajarmu Idan Ta Yi Laifi”: Bidiyon Uban Amarya Yana Yi Wa Surukinsa Nasiha Mai Tsuma Zuciya a Ranar Aurensu
"Wow ina tayaki murna faaaa. Allah kadai ne zai iya yin wannan. Shi madaukakin sarki ne Allah."
Bright Udoh ta yi martani:
"Na tayaki murna. Babu abun da Allah ba zai iya yi ba. Babu abun da aka rasa kuma babu abun da ya fashe."
Wahab Eric Oluwaseunya ce:
"Wow ina tayata da iyalinta murna. Lallai mata na da karfi."
Chialuka Chukwu ta ce:
"Yar'uwa ina maki barka da iyalinki kuma dukkan godiya ta tabbata ga Allah."
Dattijuwa mai shekaru 54 ta haifi yan uku
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Allah ya azurta wata dattijuwa da bata taba yin koda bari bane da haihuwar yara har guda uku a lokaci daya.
Asali: Legit.ng