Jami’an Hukumar Hisbah a Kano Sun Farfasa Kwalaben Barasa Na Miliyan 500

Jami’an Hukumar Hisbah a Kano Sun Farfasa Kwalaben Barasa Na Miliyan 500

  • Rahoto ya bayyana yadda aka lalata barasa da yawa a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma
  • Wannan ne karo na uku da ake yin hakan, kamar yadda kwamandan Hisbah na jihar ya fada
  • Jihohin Arewa akalla 12 ne aka haramta shigowa, siyarwa da shan barasa, mun kawo muku su

Jihar Kano - Hukumar Hisbah a jihar Kano ta lalata kayayyakin barasa da suka kai darajar Naira miliyan 500 a kwaryar jihar, The Guardian ta ruwaito.

Hisbah ta bayyana cewa, wannan ya faru ne a kokarinta na tabbatar da bin dokar haramta shigowa, siyarwa da kwankwadar barasa a jihar da ke Arewa maso Gabas.

A lokacin da ake lalata kwalaban giyan, kwamandan Hisbah, Sheikh Sani Harun Ibn-Sina ya bayyana cewa, sun lalata kayan ne daidai da umarnin kotu.

Kara karanta wannan

To fah: A kama Atiku da Peter Obi kawai, cewar jigon APC bisa muhimmin dalili

Hisbah ta lalata giya a Kano
Jihar Kano da ke Arewa maso Yamma a Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya kuma sake jaddada matsayar hukumar Hisbah wajen yaki da barna da kuma abubuwan da addinin Islama ya haramta, GistReel ta gtattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasuwancin giya na kawo kudi, Kano tana mora

Idan baku manta ba, wani rahoto a 2015 ya ce, kudaden da ake ba jihar Kano na kason harajin VAT kan kayan maye ya kai N525.74bn daga asusun gwamnatin tarayya.

Ibn-Sina ya ce:

“A jihar Kano, akwai dokar da ta haramta shigowa, siyarwa da kwankwadar barasa da sauran kayan maye.
“Don haka, za mu ci gaba da yin kokari wajen dabbaka dokar don tabbatar da an bi ta kuma jihar ta kubuta daga wadannan kayayyakin masu cutarwa.
“Ba wannan ne karon farko ba da muka dauki irin wannan matakin ba. A karon farko mun lalata ya kai kwalabe miliyan daya.

Kara karanta wannan

Ta yaya? Dan China ya amsa laifinsa, ya fadi hanyar da ya bi ya kashe Ummita

“A karo na biyu mun lalata kusan kwalabe miliyan biyu, sannan yanzu mun lalata kwalabe kusan miliyan 2.5.”

Ba a Kano kadai ake lalata barasa ba

Ba jihar Kano kadai bace ke da dokar haramta barasa, jihohin Arewa da yawa suna da irin wannan doka mai tsauri ga masu shaye-shaye.

Jihohin da ke irin wannan dokar sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Borno, Yobe, Jigawa, Bauchi, Gombe, Zamfara da Neja.

A bangare guda, kasar Saudiyya ta bayyana yiwuwar daukar mataki kan mutanen da ke zuwa aikin Hajji da Umrah amma su dage suna daukar hotuna a madadin dukufa kan ibada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.