Ya Halasta Ga Musulmai Ma’aurata Su Yi Jima’i a Cikin Watan Ramadana da Dare
- Malamin addinin Islama ya bayyana kadan daga abin da ya kamata Musulmai su mai da hankali a kai tsakaninsu da abokan zamansu a azumi
- Malamin ya ce, ya halasta Musulmi ya kusanci matarsa a watan Ramadana, amma a wani kebabben lokaci
- Musulmai a duniya na azumin watan Ramadana, daya daga cika-cikan addinin mafi yawan fadada a duniya
Abeokuta, jihar Ogun - Limamin masallacin jami’ar noma ta tarayya da ke Abeokuta, Farfesa Sherifdeen Kareem ya ce, ya halasta ma’aurata Musulmai su yi saduwar aure a cikin watan Ramadana.
Ya bayyana cewa, hakan zai yiwu ne kadai daga bayan buda-baki har zuwa cikin dare, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cewar malamin a lokacin da yake zantawa da jaridar, ya haramta ga Musulmai maza da mata su yi zina a cikin watan Ramadana ko wajensa.
Lokacin da ya halasta ma’aurata su kusanci juna
Ya kara dacewa, addinin Islama ne kadai ya ba Musulmai ma’aurata ‘yancin yin jima’i daga sallar bayan Magriba zuwa ketowar Al-fijir a lokacin azumi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
“Musulmai za su iya saduwar aure a lokacin da suka yi buda-baki, kenan bayan sallar Magriba. Matukar dai za su ci abinci, to ya halasta su taki junansu har zuwa ketowar Al-fijir.
“An ba maza damar jima’i da matansa ko mata da mazajensu daidai da ‘yancin cin abinci da shan ruwa.
“Wannan a kebe yake ga maza ma’aurata. Idan basu da aure, zina haramun ne a kowane lokaci. Don haka, addinin islama ne kadai ya ba ma’urata ‘yancin yin jima’i a azumi, tsakanin Magriba da Asuba.”
A dan nesanci juna idan ana azumi
A bangare guda, malamin ya shawarci ma’aurata Musulmai da su nesanci juna da rana idan suna azumi don gudun fitina.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ambasada Bawa ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, bayanai sun fito
A cewarsa, Annabi Muhammadu (SAW) ya sumbaci matarsa a cikin watan Ramadana, amma duk da haka ya shawarci Musulmai da su nesanci junansu da rana saboda komai zai iya faruwa.
A wannan watan na Ramadana ne Musulmai a duniya ke azumtar kwanaki 29 ko 30 a matsayin daya daga cika-cikan Musulunci.
Kira ga masu zuwa ziyarar Hajji da Umrah
A wani labarin, kasar Saudiyya ta bayyana kira ga Musulmai masu zuwa ziyara da su guji yawaita daukar hotuna a lokacin ibada.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Musulmai ke shagala da yawan dauke-dauke hotunan a ziyarar Hajji da Umrah.
Saudiyya ta ce, ya kamata Musulmai su zama masu mutunta masallatan Harami guda biyu tare da gudun aikata ‘Riya’.
Asali: Legit.ng