Abba Gida-Gida Ce Duk Masu Gini Kan Filin Gwamnati a Kano Su Gaggauta Dakatar da Aikin
- Zabebben gwamnan Kano ya shawarci wadanda suka sayi filayen gwamnati a jihar da su dakata da yin gini a kai tukuna
- Gwamnan ya ce, yana da kudurin dawo da martabar birnin Kano, don haka akwai shirin da yake dashi a kasa game da filayen
- A baya, Abba Gida-Gida ya sha sukar gwamnatin Ganduje game da batun siyar da filayen gwamnati ag daidaikun jama’a a jihar
Abba Kabir Yusuf, sabon gwamnan jihar Kano ya tura sakon gargadi da shawari mai zafi ga masu gine-gine a filayen gwamnati a duk inda suke a jihar.
A cewarsa, duk wanda ya san yana gini a kan filin gwamnati to ya dakata nan take har sai gwamnati ta sake yin magana kan lamarin.
Abba Gida-Gida ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya fitar a ranar Juma’a 31 ga watan Maris a shafinsa na sada zumunta; Facebook.
Shawarin Abba Gida-Gida ga jama’ar Kano
Sakon da ya wallafa ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Kamar yadda muka kuduri aniyar dawo da tsarin birnin Kano; Ina shawartar Jama'a da su daina duk wani aikin gine-gine na filayen gwamnati a ciki da wajen makarantu, wuraren addini da na al'adu, da dukkan asibitoci, da makabarta, da kuma gefen katangar birnin jihar Kano.”
A bangare guda, jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, mai magana da yawun zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar da sanarwa mai bayyana bayani irin wannan.
A cewar Bature, ana shawartar duk wasu da ke aikin rushewa ko gini a filayen na gwamnati to su tabbatar da sun dakata a halin da ake ciki.
Abba Gida-Gida dai ya sha bayyana sukar gwamnatin Ganduje da ke siyar da filayen jihar ta Kano ga daidaikun mutane ‘yan kasuwa a bangarori daban-daban.
An ba Abba Gida-Gida takardar shaidar lashe zabe
A wani labarin, kunji yadda aka ba Abba Gida-Gida takardar shaidar lashe zaben gwamna a jihar ta Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
A hotunan da aka yada, an ga lokacin da gwamnan ya karbi takardar tare da dandazon magoya bayansa da jam’iyyar NNPP ta su Kwankwaso.
A zaben gwamnan da ya gabata, Abba Kabir ne ya lashe zabe, inda ya lallasa Gawuna na jam’iyyar APC ta su gwamna mai barin gadi; Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Legit.ng