‘Sai Dai Mu Yi Wanke-Wanke’: Martanin Jama’a Ga Wasan Biyan Kudin Cin Abinci Da ’Yan Mata Suka Yi

‘Sai Dai Mu Yi Wanke-Wanke’: Martanin Jama’a Ga Wasan Biyan Kudin Cin Abinci Da ’Yan Mata Suka Yi

  • Tawagar wasu kyawawan ‘yan mata suna buga wasa a gidan cin abinci kan wanda zai biya kudin abincin da suka ci ya yadu
  • ‘Yan matan sun jera wayoyinsu a kan tire, inda suka nemi ma’aikaciyar gidan cin abincin ta zabi waya daya, wacce aka dauki wayarta ita za ta biya
  • Da yawan ‘yan TikTok sun yi martani mai daukar hankali kan wannan lamarin, sun bayyana idan su ne ya za su yi

Wani bidiyon tawagar ‘yan mata a gidan cin abinci suna nishadi ya sanya mutane annashuwa a kafar sada zumunta.

A lokacin da suke cikin gidan cin abincin, kawayen sun yanke shawarin buga wasan da zai ba daya daga cikinsu daman biyan kudin abincin da suka ci.

A bidiyon da @1bigfeli7 ya yada, an ga lokacin da suka nemi mai ba da abinci ta dauki wayar daya daga cikinsu, inda suka yanke duk wayar da aka dauka, mai ita ce za ta biya kudin abincin.

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Bidiyon budurwa ya girgiza matasa, ta ce ba za ta auri mai albashin N70k ba

Bidiyon 'yan mata sun ci abinci, suna jiran wa zai biya
Bidiyon 'yan mata a gidan cin abinci suna wasa | Hoto: @1bigfeli7
Asali: TikTok

Suna hannun mai ba da abinci

A lokacin da mai ba da abincin take kallon wayoyin, ‘yan matan sun natsu suna kallon tsoro. Daya daga cikinsu ta dukufa tana addu’ar kada Allah yasa a dauki wayarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikinsu ta daura hannu a ka tana ihu tare da nuna damuwar me yasa aka zabi wayarta.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa a kafar sada zumunta ta TikTok:

@Globaby:

"Ba zan yi wannan wasan ba idan har ba tare da zamu hadu mu wanke farantai ba.”

@Berrybaby:

"Ka’ida ta farko: ya zama kana da abokai masu kudi.”

@y'all meet Toria:

"Wani ya maimaita a baya na..Ba zan taba yin talauci ba a rayuwata.”

@Aderonke Salau:

"Na ga tana addu’a kafin mai ba da abincin ta dauki wayarta.”

Kara karanta wannan

Assha: Bidiyon yadda matashi ya ba budurwa damar daukar duk da abin take so a kanti cikin dakiku 30

@Annabel_18:

"Da nawa za a yi amfani wajen yin bidiyo.”

@Kekeli:

"Haka Allah zai zabe ki ya albarkace ki cikin da yawan mutane.”

@Onyebuchii:

"Ni da bani da kudi a asusu idan aka zabe ni sai dai mu hadu mu wanke kwanuka.”

@Fati_oiza:

"Idan suka zabi waya ta, rashin kudi ne zai cece ni.”

@:crown:Sefakor:

"Idan akwai Android kawai ki dauka su ne asalin masu rike kudin.”

@princessfeargod1:

"Idan aka yi wannan dani kuma aka zabi wayata lallai sai dai mu wanke kwanuka.”

@Rare_Temmah:

"Wannan wasan akwai dadi har sai an dauki wayarka.”

A wani labarin, wata budurwa ta ce ba zata auri saurayi mai samun N70,000 kadai ba a wata, ta fadi dalilinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.