Rikici Ya Barke a Siyasar APC a Bauchi Bayan da Jam’iyyar Ta Fadi a Zaben Gwamnan Jihar
- Jam’iyyar APC a jihar Bauchi ta rincabe da kalubalen rirkicin shugabanci bayan kammala zabuka a Najeriya
- Kungiyar siyasa a Bauchi ta APC Patriotic Support Group na kira ga shugaban jam’iyyar a jihar, Babayo Misau da ya yi murabsu
- Da yake magana a madadin kungiyar, Almustapha Zubairu ya ce, manufar tagawar itace kira ga shugabanni game da matsalolin da APC ke ciki a Bauchi
Jihar Bauchi – Biyo bayan rasa kujerar gwamna a jihar, jam’iyyar APC ta dare a Bauchi, inda rikici ya kunno kai mai dumi.
A cewar rahoton jaridar Tribune Online, rikicin ya kai ga an fara neman shugaban APC na Bauchi da ya gaggauta sauka daga kujerarsa.
Wannan batu na neman tsige shugaban APC na Bauchi, Babayo Misau na zuwa ne a cikin wata wasika da kungiyar APC Patriotic Support Group ta sake a Bauchi.
Rikicin da ya kunno kai a APC a Bauchi
Wasikar an tura ta ne ga zababben shugaban kasa na Najeriya, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da kungiyar ke jawabi a jihar Bauchi a ranar Laraba 29 ga watan Maris, ta ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa domin ceto jam’iyyar.
Almustapha Zubairu, wani mamban kungiyar ya ce, ya yi magana ne a madadin da yawan mambobin kungiyar, inda ya bayyana manufar da suke son cimmawa.
Akwai bukatar a dauki mataki
Zubairu ya bayyana cewa, akwai bukatar mai da hankali ga halin da jam’iyyar ke ciki na bakin rashin lafiya, kuma dole a jawo hankalin shugabanni.
A cewarsa, yin magana da daukar matakin ne zai dawo da kwarin gwiwar ‘ya’yan jam’iyyar a jihar da kuma mutunta kundin tsarin mulkinta.
Jam’iyyar APC dai ta gaza cin zabe a jihar Bauchi, lamarin da ya jawo cece-kuce a jam’iyyar da kuma barkewar rikicin cikin gida.
Jam'iyyar APC Za Ta Titsiye Sanata Da Wani Dan Majalisar Wakilai Daga Jihar Gombe Bisa Zargin Cin Dunduniyar Jam'iyya
Akwai masu kitsa hanyar kafa gwamnatin wucin gadi, DSS ta magantu, PDP da APC sun ba da shawari
A wani labarin, kun ji yadda jam’iyyun APC da PDP suka hada kai wajen ba hukumar tsaro ta DSS shawari kan wani lamari mai sarkakiya.
Ana zargin wasu ‘yan siyasa a Najeriya da kokarin kitsa yadda za su kafa gwamnatin wucin gadi kafin rantsar da Bola Ahmad Tinubu.
A cewar PDP da APC, ya kamata a bayyana sunayen ‘yan siyasan tare da kame su don daukar matakin doka da ya dace.
Asali: Legit.ng