Wani Basarake a Jihar Gombe Ya Rasa Biyu Daga Cin Yan Uwansa a Hatsari

Wani Basarake a Jihar Gombe Ya Rasa Biyu Daga Cin Yan Uwansa a Hatsari

  • Galadiman Tangale kuma hakimin Bare a jihar Gombe, Alhaji Yunusa Adamu Fawu, ya yi babban rashin iyalansa mutum 2
  • Matar hakimin da ɗan yayansa ne suka rasu a wani haɗari mara kyau da ya rutsa da su hanyar zuwa Kaduna
  • Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi ta'aziyya tare da tura ƙusoshin gwamnati ta'aziyya har gida

Gombe - Biyu daga cikin iyalan gidan Galadiman Tangale a jihar Gombe, Alhaji Yunusa Adamu Fawu, sun rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da su.

Hatsarin ya rutsa da yan uwan fitaccen Basaraken ne yayin da suke kan hanyar zuwa jihar Kaduna domin kai ziyara.

Hadarin Mota.
Wani Basarake a Jihar Gombe Ya Rasa Biyu Daga Cin Yan Uwansa a Hatsari Hoto: leadership

Bayanai sun nuna cewa Galadiman Tangale shi ne hakimin Bare da ke ƙaramar hukumar Billiri a jihar Gombe, arewa maso gabashin Najeriya.

Mutanen biyu da suka rasu a haɗarin sun haɗa da Adamu Mohammed Fawu, mai shekara 35 a duniya, ɗan yayan hakimin Bare, Mohammed Adamu Fawu, kuma jami'in hukumar kiyaye haɗurra (FRSC).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: DSS Ta 'Gano' Manyan Yan Siyasa Da Ke Shirin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Gabanin Mika Wa Tinubu Mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma matar hakimin, Hussaina Yunusa Adamu, yar kimanin shekaru 41 a duniya, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Gwamnan Gombe ya yi ta'aziyya

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan gidan Sarautan bisa wannan babban rashi na 'yan uwansu biyu.

Inuwa Yahaya ya tura manyan wakilai karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Dakta Manassah Daniel Jatau, waɗanda suka je gidan hakimin Bare suka yi ta'aziyya a madadin gwamnati.

"Lokacin da muke jin raɗaɗin tafiyar wasu masoyanmu, ya kamata mu tuna da Allah mu rungumi kaddara, mu gaskata Ubangiji zai yaye ciwo da radaɗin da muke ji."
"Allah ya sauƙaƙa mana hanyar waraka domin lokaci kaɗai ya isa ya yaye mana damuwar da muka shiga, idan aka ɗauki wani lokaci zamu manta da ƙuncin da muka shiga.

- Mataimakin gwamna Jatau.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Sabuwar Rijiyar Mai Ta Jihar Nasarawa

Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Rasa Kwamshinan Harkokin Addinai

A wani labarin kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya rasa kwamishinansa guda ɗaya

Kwamishinan harkokin addinai, Alhaji Usman Suleiman (Ɗanmadamin Isa), ya rasu yana da shekaru 72 a duniya.

Kafin rasuwarsa ya rike manyan mukamai a gwamnati da kuma jam'iyyarsa ta PDP amma ya cika yana kan kujerar Kwamishina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262