Ya Kamata a Ba Kudu Maso Kudu Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, Mataimakin Shugaban APC
- Jigon jam’iyyar APC ya bayyana bukatar a ba Kudu maso Kudu damar gaje kujerar shugaban majalisar dattawa ta kasa
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kowa ke bayyana cancantarsa wajen gaje wannan kujera mai daraja a Najeriya
- A baya, Abdulaziz Yari ya ce yana da burin gaje Ahmad Lawal idan za a bashi dama, ya fadi dalilansa na fadin haka
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa daga yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya bukaci jam’iyyar ta mika kujerar shugaban majalisar dattawa zuwa yankin Kudu maso Kudu, Channels Tv ta ruwaito.
Lukman ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar da ya fitar a ranar Laraba 29 ga watan Maris, inda ya bayyana yadda a baya tsarin shiyya ya yi amfani wajen shugabancin majalisar.
Ya kuma yi gargadin cewa, tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi na Tinubu da Shettima zai iya shafar shugabancin majalisar, matukar aka ba Musulmi.
Dalilin da zai sa a ba Kudu maso Kudu kujerar
Ya bayyana cewa, ya kamata ‘yan Kudu maso Kudu su samu wannan damar, inda yace ‘yan yankin sun ba APC kuri’u a zaben da ya gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ra’ayinsa, ya kuma ce ya kamata a ba Kudu maso Gabas kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa.
Jigon na APC ya ce, bai kamata mutanen Arewa maso Yamma su fara nuna sha’awarsu ga wannan kujerar ba tare da tuntubar kwamitin ayyuka na jam’iyyar ba.
‘Yan Arewa su yi hakuri
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar daga yankin Arewa maso Yamma da su janye muradunsu na gaje kujerar ta Ahmad Lawal don ba jam’iyyar daidaiton raba mukamai.
‘Yan siyasa da yawa ne daga Arewa maso Yamma suka bayyana sha’awar gaje Ahmad Lawal a wannan karo, inda suka bayyana hujjojinsu, rahoton TheCable.
Hakazalika, idan baku manta ba an kai ruwa rana bayan da Tinubu ya bayyana zaben Shettima a matsayin mataimakinsa, lamarin da ya keta tsakanin APC.
Yari na son zama shugaban majalisar dattawa
A wani labarin, kun ji yadda tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana sha’awarsa ta zama shugaban majalisar dattawa nan ba da jimawa ba.
Yari y ace, ya kamata a ba Arewa maso Yamma wannan dama ta samar da shugaban majalisa saboda wasu dalilai.
Hakazalika, ya nemi goyon bayan jiga-jigan siyasar yankin, inda yace shine ya cancanta a ba wannan dama ta jagorantar majalisar ta 10.
Asali: Legit.ng