Gwamna Zulum Na Borno Zai Sake Gina Wasu Kauyuka 3, Buhari Ya Ba Shi N15bn Na Aikin

Gwamna Zulum Na Borno Zai Sake Gina Wasu Kauyuka 3, Buhari Ya Ba Shi N15bn Na Aikin

  • Gwamna Zulum ya ce zai sake gina wasu kauyuka uku a jiharsa da ‘yan ta’adda suka lalata a shekarun baya
  • Tun 2014 ake fatattakar mazauna yankunan jihar Borno da Yobe, lamarin da ya daidaita matsugunan jama’a
  • Gwamnan ya gana da kwamitin shugaban kasa, an ba shi kudin don yin wannan babban aikin ga al’ummar Borno

FCT, Abuja - Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno ya bayyana aniyarsa ta sake gina wasu kauyuka uku da ‘yan ta’addan Boko Haram suka lalata a jihar.

A cewar Zulum, wannan aikin zai taimaka wajen dawo da ‘yan gudun hijirar da suka tsere suka bar muhallansa sakamakon barnar ‘yan ta’addan.

Jihohin Arewa maso Gabas, musamman Borno da Yobe suna shan fama da barnar ‘yan Boko Haram, inda tsagerun suka raba mutane sama da 20,000 da muhallansu a jihohin.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan bindiga na neman fansan miliyoyi kan jami'an INEC da suka sace a jihar Arewa

Gwamna Zulum zai yi aikin gina kauyuka a Borno
Gwamna Zulum a lokacin da ya gana da shugaba Buhari | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, da yawan ‘yan gudun hijiran sun yi kaura ne zuwa kasashen Nijar, Kamaru da Chadi da ke makwabtaka dasu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sabon aikin da Zulum zai yi a Borno

Da yake bayyana abin da ya sa a gaba na gini a kauyukan, Zulum ya yada wata sanarwa a Twitter, inda yace ‘yan Boko Haram sun raba jama’arsa da matsugunansu tun 2014.

A cewar sanarwar, Zulum ya bayyana wadannan kalaman ne a lokacin da yake tattaunawa da kwamitin dawo da ‘yan gudun hijara garuruwansu a Abuja.

Idan baku manta ba, Zulum ne mataimakin shugaban kwamitin shugaban kasa kan harkokin gudun hijra da maido da wadanda aka daidaita zuwa muhallansu da ke rayuwa a kasashen keyare.

Kadan daga aikin kwamitin shugaban kasa

Hakazalika, kwamitin na mai da hankali ga dawo da tubabbun ‘yan ta’adda kan turba ta gari a duk sadda suka mika wuya ga sojoji ko wasu jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

A bangare guda, mataimakin shugaba, farfesa Yemi Osinbajo ne shugaban kwamitin na shugaban kasa kan maido da ‘yan gudun hijira matsunansu.

Game da kudaden da za a kashe wajen ginin, tuni Zulum yace shugaba Buhari ya amince da sakin N15bn domin yin wannan aikin a jihar ta Borno.

A wani labarin, kun ji yadda ‘yan ta’addan ISWAP suka sha luguden wuta daga sojojin Najeriya bayan kammala zaben gwamna a jihar ta Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.