Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Jindadin 'Yan Sanda Ta Ƙasa

Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Jindadin 'Yan Sanda Ta Ƙasa

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon shugaban hukumar jindaɗin ƴan sanda ta ƙasa
  • Solomon Arase ya kama aiki a yau watanni biyu bayan majalisar dattawa ta amince da naɗin da aka yi masa
  • Sabon shugaban hukumar ya sha alwashin daƙile cin hanci da rashawa a rundunar ƴan sandan Najeriya

Abuja- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon sufeta janar na ƴan sandan Najeriya, Solomon Arase (rtd), a matsayin sabon shugaban hukumar jindaɗin ƴan sanda ta ƙasa (PSC)

Sabon shugaban hukumar yayi rantsuwar kama aiki ne a ranar Laraba a ɗakin taron majalisar zartarwa ta ƙasa jim kaɗan kafin a fara taron majalisar zartarwas. Rahoton Channels Tv

Arase
Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Jindadin 'Yan Sanda Ta Ƙasa Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Rantsuwar ta sa na zuwa ne watanni biyu bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

Matashiya: Yadda Jami'ar Chicago ta Tabbatar da Cewa Makarantar Tinubu Ya Halarta

Daga cikin waɗanda suka halarci wajen taron ƙaddamarwar akwai mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da sauran su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Arase wanda yayi ritaya a shekarar 2016, shine sufeto janar ɗin ƴan sanda ɗan Najeriya na goma sha takwas (daga watan Afrilun 2015 zuwa watan Yunin 2016). Yayi aiki a wurare da dama a rundunar ƴan sandan Najeriya.

A wata hira da ƴan jaridan fadar gwamnatin tarayya, Arase yayi alƙawarin bai wa jindaɗin jami'an rundunar ƴan sandan cikakken muhimmancin da ya dace.

Ya kuma sha alwashin kawar da matsalar cin hanci da rashawa da rigingimun dake ta faruwa tsakanin IGP da hukumar PSC.

Kungiyar Kwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba CBN Wani Sabon Wa'adi

A wani labarin na daban kuma, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta fasa gudanar da yajin aikin da ta shirya gudanar wa a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ƙwadagon a da ta shirya gudanar da yajin aiki a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Masha Allah: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rijiyar Hakar Man Fetur a Jiha Ta 2 a Arewacin Najeriya, Ta Bayyana Burin Ta Akan Rijiyar

Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewa ta janye wannan yajin aikin da ta shirya gudanarwa, amma ba gabaɗaya ba inda tace zata jira ne na wani ɗan lokaci domin ganin yadda lamura za su kaya.

Ƙungiyar ƙwadagon da zata yi yajin aikin ne saboda ƙarancin kuɗi da ake fama da shi a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng