Dakatar da Ayu Ya Saba Dokar Jam’iyyarmu, Tawagar Kamfen Shugaban Kasa Na PDP Ta Magantu
- Tawagar kamfen din takarar shugaban kasa ta PDP ta bayyana fushinta game da dakatar da shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu
- An dakatar da Ayu tare da maye gurbinsa da wani saboda wasu rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar ta PDP
- PDP PCC ta ce, dakatar da Ayu ya saba doka, kuma hukuncin kotu na hana Ayu din aikinsa babban abin tashin hankali ne
FCT, Abuja - Tawagar gangamin takarar shugaban kasa na PDP ta ayyana dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu a matsayin haramtaccen aiki da ya saba kundin dokar jam’iyyar, Vanguard ta ruwaito.
Wannnan na fitowa ne daga bakin kakakin tawagar Mr Charles Aniagwu a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na AIT a ranar Talata.
A cewarsa, wadanda suka datakarar da Ayu sun jahilci kundin tsarin dokar jam’iyyar PDP da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 2017.
Abin da ya faru a PDP ya faru a APC
Charles ya jaddada cewa, dakatar da shugaban na PDP daidai yake da abin da ya faru da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole a lokacin da yake shugaban APC na kasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da yake cewa kundin tsarin tafiyar da jam’iyyar APC na da bambanci da PDP, ya kara da cewa, babu wadanda ke da ikon dakatar da shugaban jam’iyya sai kwamitin ayyuka na jam’iyyar.
A cewarsa:
“A bayyana balo-balo a sashe na 57(7) a kundin PDP game da wanda ke da ikon dakatarwa ko ladabtar da mamban kwamitin ayyuka ko kwamitin shugabanni na jam’iyyar.”
Kotu ya yi kuskure a hukuncinsa
Charles ya kara da cewa, umarnin kotu na hana Ayu ci gaba da tafiyar da harkokinsa na shugabancin PDP babban abin takaici ne, inda yace akwai kuskure a hukuncin na kotu.
Sai dai, ya bayyana kwarin gwiwarsa da cewa, jam’iyyar za ta fito da karfinta bayan warware dukkan matsalolin da take ciki a halin yanzu, Daily Trust ta ruwaito.
Tun farkon nada Ayu da zabo Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP ake ci gaba da kai ruwa rana da samun sabani a jam’iyyar.
An samu ballewar wasu gwamnoni biyar, wadanda suka ce ba za su goyi bayan Atiku a zaben shugaban kasa ba har sai an tsige Ayu.
Asali: Legit.ng