“Akwai Dadi”: Matashiya Mai Mazaje 2 Ta Ce Suna Biya Mata Bukatunta Daban-Daban

“Akwai Dadi”: Matashiya Mai Mazaje 2 Ta Ce Suna Biya Mata Bukatunta Daban-Daban

  • Carl da Tiger sun kasance mazajen Kenya wacce ke matukar son yin soyayya da mutum fiye da daya kuma tana neman karin mazaje
  • Kenya da mijinta na farko Carl sun shekara 12 da aure kafin suka yanke shawarar shigo daTiger rayuwar aurensu
  • A cewar Kenya, wani bangare na rayuwarta da ya shafi tunani ya yi daidai da Carl yayin da daya bangaren da ke son jindadi da sharholiya ya yi daidai da Tiger

Yayin da wasu matan ke neman kyawawan jaruman maza da za su kira da nasu, Kenya ta rigada ta mallaki zaratan maza har guda biyu wadanda suke mallakinta.

mata da mazajenta su biyu
“Akwai Dadi”: Matashiya Mai Mazaje 2 Ta Ce Suna Biya Mata Bukatunta Daban-Daban Hoto: Progressive _Love_ Academy.
Asali: Instagram

Kenya da Carl sun shafe shekaru 12 da aure

Kenya da mijinta na farko, Carl, sun shafe shekaru 12 da aure lokacin da ta fada tarkon son wani santalelen saurayi mai suna Tiger kuma ta gabatar da shi a rayuwar aurensu.

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Jama'a sun kadu bayan ganin mutumin da ya reni zakanya tsawon shekaru 11

"Ni da Carl mun yanke shawarar cewa zan auri namiji fiye da daya saboda na hadu kuma na fada tarkon son wani gaye," in ji Kenya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun yanke shawarar yin magana kan haka, muna al'ajabin mai ya kamata mu yi, yaya za mu bi da lamarin?" Carl ya tambaya.
"Mun tattauna kan haka tsawon shekaru sannan muka fahimci maganganun mata, za ka ga cewa ya zama dole ka bar mata su fadi abun da ke ransu sannan su zamo masu yanci," in ji Carl.

Kenya ta hadu da Tiger a wajen liyafa

Kenya da Tiger sun hadu a wani liyafa sannan suka fara rawa sai kuma Tiger ya yanke shawarar bibiyarta.

“Ina da abubuwan ban mamaki, Ina ji kamar Carl ya yi daidai da wani bangare nawa; da ya shafi tunani, kuma muna irin tattaunawar nan mai zurfi sannan daya bangaren shine son jin dadi, sharholiya, tafiye-tafiye kuma a nan ne muka dace da Tiger. Ni dukka mutanen biyu ce, Ina son mallakar abokan rayuwa da yawa,” in ji Kenya a shafin ET na YouTube.

Kara karanta wannan

“MIliyan 3 Zan Sayar” : Wani Mutum Daya Fito da Dadaddiyar Mota Samfurin “1974 Volkswagen Beetle”

Su dukka ukun suna da abubuwa na musamman a tattare da su kuma suna tallafawa junansu.

“A shirye nake na tallafawa Tiger da Kenya a duk lokacin da suke bukatar haka a soyayyarsu ko ma a wani abu na daban,” in ji Carl.

A cewar Tiger, mutane da dama na mamakin dalilin da zai sa namiji ya yarda da wani namijin a gidansu amma sun yarda da hakan domin suna kallonsa a matsayin abu mai kyau.

“Akwai dadi, duk muna son kulawa da karfi,” in ji Kenya.

Budurwa yar shekaru 20 ta koka saboda rashin manemi

A wani labari na daban, mun ji cewa wata budurwa yar shekaru 20 ta garzaya soshiyal midiya don bayyana halin da take ciki na rashin mashinshini duk da cewar ta kai budurwa son kowa kin wanda ya rasa.

Budurwar wacce ta zubar da hawaye ta ce bata da wanda ke daukar dawainiyariya domon

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng