Gwamnatin Tarayya Tayi Magana Kan Zanga-Zangar Da NLC Ta Shirya

Gwamnatin Tarayya Tayi Magana Kan Zanga-Zangar Da NLC Ta Shirya

  • Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa sun daƙile batun zanga-zangar da ƙungiyar NLC ta shirya
  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa tayi barazanar tsunduma cikin zanga-zanga a faɗin ƙasar nan kan ƙarancin kuɗi
  • Ministan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta shawo kan wannan matsalar

Abuja- Ministan Ƙwadaho da samar da aikin yi, Chris Ngige, ya bayar da tabbacin cewa sun daƙile barazanar zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) kan babban bankin Najeriya (CBN) bisa ƙarancin takardun kuɗi. Rahoton The Nation

Ƙungiyar ƙwadagon ta ƙasa ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwana bakwai kan ta sanya CBN da bankunan kasuwanci su kawo ƙarshen ƙarancin kuɗin, wanda idan ba haka ba tayi gargaɗin yin zanga-zanga a faɗin ƙasar nan da kuma mamaye rassan bankin CBN.

Kara karanta wannan

"Na Sama Da Mu Sun Karbi Tuhumar", 'Yan Sanda Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki Game Da Shari'ar Ado Doguwa

Kwadago
Gwamnatin Tarayya Tayi Magana Kan Zanga-Zangar Da NLC Ta Shirya Hoto: The Nation
Asali: UGC

Sai dai da yake jawabi a wajen bayar da bayanin ministiri na mako-mako wanda ake gudanarwa a birnin tarayya Abuja, ministan yace an shawo kan matsalar.

Mr Chris Ngige ya bayyana cewa ministirin sa ta shirya tattaunawa domin ganin babban bankin Najeriya (CBN) ya ɗauki matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan wanda ya samu rakiyar ƙaramin ministan ƙwadago da samar da aikin yi, Festus Keyamo, da wasu sauran manyan jami'an ministirin, yace a halin yanzu maganar zanga-zanga bata daga cikin abinda NLC zata tattauna akai a taron da zata yi.

Ministan ya bayar da tabbacin cewa tuni aka kawar da maganar zanga-zangar da ƙungiyar ta shirya.

"Yanzu sun amsa kiraye-kirayen da muke musu domin muna sarakan samar da sasanci. Tun da farko a wajen jawabina na bayyana cewa akwai tattaunawar dake gudana, sannan ƙungiyar ƙwadago ta amince akwai huɓɓasar da ake yi domin kawo ƙarshen matsalar."

Kara karanta wannan

An Tafka Magudi: Dan Takarar Gwamnan PDP Yaki Yarda Da Kaddara, Zai Kalubalanci Sakamakon Zabe a Kotu

Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka Daga Kujerarsa, An Maye Gurbinsa

A wani labarin na daban kuma, shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa yayi murabus daga kan muƙamin sa na shugabancin jam'iyyar.

Sanata Iyorchia Ayu, yayi murabus daga kan muƙamin sa na shugabancin PDP inda tuni har an maye gurbin sa da wani daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng