"Namiji Na So Na Haifa a Farko" Wata Mata Ta Barke da Kuka Bayan Ta Haihu a Bidiyo
- Wata sabuwar mai jego, wacce ba ta jima da sauka ba, ta zubda hawaye bayan ta haifi mace, tace Namiji ta so a matsayin ɗan fari
- A wani bidiyo da aka wallafa a Soshiyal midiya, matar ta ce ta jima tana mafarkin haihuwar ɗa namiji a karon farko
- Amma bisa yadda Allah ya so, matar ta haifi ɗiya mace kuma an ga Mijinta na rarrasahi ta daina kuka kan juyawar lamarin
Wata matar aure 'yar Najeriya wacce ba ta jima da haihuwar fari ba, ta shiga damuwa saboda jaririn da ta haifa ya kasance mace.
A wani bidiyo da shafin @gossipmilltv, ya wallafa a Instagram, sabuwar mai jegon ta kama kuka tana zubda hawaye daga idanuwanta.
A cewarta, a ko da yaushe burinta da mafarkinta shi ne ta haifi ɗa namiji a matsayin ɗan fari a rayuwarta.
Maimakon Namiji Allah ya ba ta mace
A cikin Bidiyon, matar ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A ko da yaushe burina na haifi namiji a matsayin ɗan fari amma 'yar kyakkyawar gimbiyata ta zabi zuwa a farko."
A ɓangaren mijinta kuwa ba haka yake kallon lamarin ba, ya bayyana cewa duk ɗa ai ɗane ba tare da tsayawa tantance wane jinsi bane.
Ya faɗa wa sahibar tasa ta daina kuka tana zubda hawayenta, inda ya tabbatar mata da cewa ɗan da zasu haifa na gaba zai kasance namiji.
Bidiyon ya yi yawo kuma ya haddasa cece-kuce, masu amfani da dandalin Instagram sun yi martani kan abinda ya faru da matar.
Duba bidiyon a nan
Martanin jama'a
@gylliananthonette ya ce:
"Wasu na can na Addu'ar Allah ya ba su haihuwa ko wane jinsi ne, ko da yaushe ki kasance mai godiya."
"Zan Koma Gida": Wata Yar Najeriya Ta Sharɓi Kuka A Bidiyo Mai Ratsa Zuciya, Ta Ce Ta Gaji Da Aiki A Dubai
@carphy_flinks ta ce:
"Ki bani idan baki so."
@endylight1 ta ce:
"Ki gode Allah, wannan shi ne albarka ta farko, ki yarda da ni mata sun fi kula da iyayen su, Namiji zaki haifa na gaba."
A wani labarin kuma 'Da Ya Sayar Da Mahaifinsa Mai Shekaru 82 Ga Matsafa Kan N1.8m A Ekiti
Wata Kotu a jihar Ekiti ta aika da wasu mutane uku gidan gyaran halin zarginsu da yin garkuwa da dattijo dan kimanin shekara 82 a duniya.
An zargi babban wanda ake kara da sace dattijon na tsawon makonni daga busani kuma aka gano gawarsa.
Asali: Legit.ng