Mutumin da Ya Reni Zakanya Na Tsawon Shekaru 11 Ya Yadu a Intanet, Jama’a Suna Ta Mamaki

Mutumin da Ya Reni Zakanya Na Tsawon Shekaru 11 Ya Yadu a Intanet, Jama’a Suna Ta Mamaki

  • Wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta na yadda wani mutum ya fito da zakanyar da ya rena na tsawon shekaru 11
  • A cikin bidiyon, an ga lokacin da mutumin ke tafiya da kafceciyar dabbar kana yana wasa da ita, suna zaune a wuri daya
  • Jama’ar kafar sada zumunta na TikTok sun cika da mamaki, sun yi martani mai daukar hankali game da wannan mutumin

A wani bidiyon da ya yadu a kafar TikTok, an ga wani mutumin da yace ya kiwata zakanya na tsawon shekaru 11, ya nuna yadda take kwaikwayarsa.

A bidiyon da @sirgathelioness ya yada, an gan shi yana zaune a gefen zakanyar ba tare da wani tsoro ba, ko gezau.

Mutumin ya bayyana cewa, yana yiwuwa mutane su samu karbuwa da sabo a idon dabbobi masu farauta irin zakuna kuma su zauna tare.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

Yadda wani ke wasa da zakanya ya ba da mamaki
Mutumin da ya reni zakanya tsawon shekaru 11 | Hoto: @sirgathelioness
Asali: TikTok

Shekaru 11 ina tare da zakanya, inji mutumin

Mutumin ya bayyana cewa, a yanzu haka ya shafe shekaru 11 yana tare da wannan zakanyar, kuma yana mata kallon daya daga cikin ahalinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, mutane sama da 3000 ne suka yi tsokaci game da bidiyon mutumin mai ban mamaki.

Legit.ng ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa game da labarin mutumin, ga kadan daga ciki.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@Democracy_Killed_Socrates:

"Ina ganin zakuna sun fi zama dabbobi masu sabo da mutane, abin ya ba da ma’ana shine yadda zaki ke alakantuwa mai karfi da mai ba shi kula.”

@Kowalski:

"Kyakkyawar zakanya, abin alfahari, ina jinjina. Za a yi kewarsu idan aka hallaka su.”

@Snow blower:

"Da fari ka ba su kulawa, sannan su ma su ba ka kulawa.”

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

@Christian:

"Zaki. Wannan kyakkyawan abu ne mai kyan gani.”

@user35737474:

"Na tabbata mai zakin ya fi wadanda ke yanar gizo sanin hadarin da ke tattare dashi.”

@dabi_wife:

"Ina ma zan zama abokiya ga zaki.”

@Jet-Machine_R/X:

"Ba komai bane batu ne na mutuntawa.”

@Zaddy_goku:

"Ga wadanda ke mamakin me yasa zakanyar bata cinye shi saboda tana masa kallon shi ne mahaifanta kuma dai zakuna ba sa cin iyayensu.”

@Spicybigtoeenchilada:

"Idan wani abu ya so farmakarsa zakin zai kare shi dari bisa dari.”

Haka nan, wani bidiyo ya nuna yadda wata 'yar Najeriya ke tafiya da zakuna abin sha'awa, jama'a sun yi martani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.