Gwamnan CBN Ya Roki NLC Ta Janye Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Karancin Nairs

Gwamnan CBN Ya Roki NLC Ta Janye Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Karancin Nairs

  • Gwamnan CBN ya roki ƙungiyar kwadugo ta kasa NLC ta janye shirinta na fara zanga-zanga ranar Laraba kan karancin naira
  • Emefiele ya gana da shugabannin NLC karkashin shugabancin Ministan Kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige
  • NLC ta umarci mambobinta su mamaye duk wani bankin CBN da ke faɗin Najeriya daga ranar Laraba mai zuwa

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ranar Litinin ya roki ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya rarrashi kungiyar kwadugo (NLC).

Daily Trust ta tattaro cewa Emefiele ya bukaci Ngige ya taimaka ya sa baki NLC ta janye zanga-zangar da ta shirya farawa ranar Laraba mai zuwa a faɗin kasar nan.

Zanga-zangar NLC.
Gwamnan CBN Ya Roki NLC Ta Janye Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Karancin Naira Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Idan baku manta ba ranar Jumu'an da ta shige, shugabannin NLC suka umarci dukkan mambobinsu su mamaye rassan CBN da ke faɗin Najeriya kan karancin tsabar kuɗi.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

Amma a wani taron sirri da ya gudana a Shalkwatar ma'aikatar kwadugo da ke Abuja, an ji Emefiele na cewa zanga-zangar zata jiƙa wa CBN aiki idan ba'a dakatar da ita ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban NLC ga jagoranci shugabannin kungiyar kwadugo yayin da Emefiele ya jagoranci tawagar CBN zuwa wurin taron wanda Ministan Kwadugo ya jagoranta.

Wani jami'in ma'aikatar, wanda ya halarci taron ya shaida wa jaridar Vanguard cewa Emefiele ya yi alkawarin CBN zai baiwa bankunan kasuwanci isassun takardun naira.

"Kun san cewa a ranar Jumu'a da ta gabata CBN ya umarci bankuna sun fito aiki a ranakun karshen mako domin sauƙaƙa kuncin karancin kuɗi a hannu."
"Gwamna ya zo ne domin ya yi magana da Minista a rarrashi shugabannin kwadugo. Ya ce zanga-zangar zata tsaida abubuwa cak a bankin, shiyasa na amsa kiran Minista, babban mai shiga tsakani."

Kara karanta wannan

Ka kawo karshen yunwa da fatara: Kungiyar Musulmai ta roki Tinubu alfarma idan ya karbi mulki

Babu ko ɗaya daga cikin bangarorin uku da ya zamta da 'yan jarida bayan fitowa daga taron sirrin. Amma a wata gayyata da ake aike mana, shugaban NLC ya ce zai yi jawabi gobe Talata.

CBN Na Shirin Dakatar da Ayyukan Bankuna 2 a Najeriya Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

A wani labarin kuma CBN ya karyata labarin da ke yawo cewa ya gama shirin dakatar da ayyukan OPAY da Palmpay a Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun CBN, Isa Abdulmumini, ya fitar, ya ce labarin bai da kamshin gaskiya a cikinsa.

Haka zalika bankunan Intanet ɗin sun fitar da sanarwa ta musamman kan batun daina aiki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262