Jihar Gombe Ta Zama Ta Farko a Jerin Inda Ake Kasuwanci Cikin Sauki a Najeriya

Jihar Gombe Ta Zama Ta Farko a Jerin Inda Ake Kasuwanci Cikin Sauki a Najeriya

  • Jihar Gombe ta zama ta ɗaya a cikin jerin jihohin da gudanar da harkokin kasuwanci yake da sauƙi a Najeriya
  • Wannan na ƙunshe ne a cikin wani sabon rahoto da ya bayyana kan gudanar da harkokin kasuwanci a sauƙaƙe
  • Baya ga jihar Gombe, jihohin Arewacin Najeriya biyu, Jigawa da Sokoto ne suka zo na biyu da na uku a cikin jerin

Abuja- An sanya jihar Gombe a matsayin jiha ta farko a cikin jerin jihohin da ake samun sauƙin gudanar da kasuwanci a Najeriya, a wani rahoto da Presidential Enabling Environment Council (PEBEC) ya fitar.

Wannan shine karo na biyu da jihar Gombe ke zuwa a matakin farko a cikin jerin. Rahoton The Cable

Gombe
Jihar Gombe Ta Zama Ta Farko a Jerin Inda Ake Kasuwanci Cikin Sauki a Najeriya Hoto: The Cable
Asali: UGC

Jihar ta zo ta farko lokacin da PEBEC ya saki rahoton sa na farko kan samun sauƙin kasuwanci a watan Maris 2021.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: 'Yan Sanda Sun Fallasa Fuskokin Mutane 17 da Aka Kama Lokacin Zaɓe a Nasarawa

A cewar sabon rahoton na PEBEC, jihar Gombe ta samu ɗigo 7.15 inda ta zama jiha ta ɗaya da ake yin kasuwanci a sauƙaƙe, yayin da jihar Jigawa ta zo jiha ta biyu inda ta samu ɗigo to 6.88, sannan sai jihar Sokoto ta zo ta uku inda ta samu ɗigo 6.79.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

PEBEC, a cikin wata sanarwa tace, rahoton yayi la'akari da wasu abubuwa shida, kayayyakin aiki, wuri mai tsaro, samun bayanan gaskiya, muhalli mai tafiya akan tsari, ma'aikata da kuma samun damarmakin kasuwanci. Rahoton Leadership

Majalisar ta PEBEC ta bayyana cewa kowace jiha an aunata ne a sikelin 1-10 akan waɗannan ma'aunan, wanda hakan ya samar da abinda akayi amfani da shi wajen samo alƙaluman sauƙin yin kasuwanci na kowace jiha na shekarar 2023.

Idan aka yi duba kan rahoton zuwa yankunan ƙasar nan, jihar Plateau ta zo ta ɗaya a yankin Arewa ta Tsakiya da ɗigo 5.8, jihar Gombe ta zo ta ɗaya da ɗigo (7.15) a yankin Arewa maso Gabas, jihar Jigawa ta zo ta ɗaya a yankin Arewa maso Yamma da ɗigo (6.88).

Kara karanta wannan

CBN Na Shirin Dakatar da Ayyukan Bankuna 2 a Najeriya Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

Jihar Anambra mai ɗigo (6.19) ta zo ta farko a yankin Kudu maso Gabas, jihar Rivers da ɗigo (5.76) ta zo ta farko a yankin Kudu maso Kudu sannan sai jihar Ekiti ta ke akan gaba a jihohin yankin Kudu maso Yamma da ɗigo (5.79).

PEBEC tace an shirya rahoton ne domin samar da cikakken bayani kan janyo hankalin harkokin kasuwanci zuwa jihohi da kuma zama wani gagarumin abin kallo ga harkokin kasuwanci da masu zuba jeri.

CBN Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin da Yasa Ya Kirkiri Manhajar eNaira da Kuma Tasirinta

A wani labarin na daban kuma, babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana dalilin sa na samar da sabuwar manhajar nan ta eNaira.

Babban bankin na CBN ya kuma bayyana tasirin ta ga tattalin arziƙin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng